Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Ya Karyata Cewar Hukumar ICPC Ta Kama Shi

Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Ya Karyata Cewar Hukumar ICPC Ta Kama Shi

  • Dan takarar gwamnan APC a jihar Sokoto ya yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama shi kafin ta sako shi
  • Ahmded Aliyu Sokoto ya ce abokan hamayya wadanda suka firgita da shahararsa a jihar sune suka kagi wannan labari na kanzon kurege
  • An dai ji cewa hukumar ICPC ta kama dan takarar kan badakalar naira biliyan 12 da ake zarginsa a kai lokacin da yake sakataren asusun lamuni na yan sanda

Sokoto - Dan takarar gwamnan jihar Sokoto karkashin iniwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ahmed Aliyu Sokoto, ya karyata batun cewa hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gayyace shi ko ta kama shi don amsa tambayoyi.

Yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a yankin Mabera da ke jihar a yammacin ranar Asabar, Aliyu ya karyata cewar aka kama shi saboda aikinsa yayin da yake sakataren asusun lamuni na yan sanda, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Zan Bayar Da Ilimi Kyauta Idan Na Zama Gwamnan Kano - Abba Gida-gida

Ahmed Aliyu Sokoto
Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Ya Karyata Cewar Hukumar ICPC Ta Kama Shi Hoto: Punch
Asali: UGC

Idan za ku tuna, wasu kafafen watsa labarai sun yi zargin cewa ICPC ta tsare jigon na APC kan badakalar naira biliyan 12 kafin aka bayar da belinsa.

Rahoton ya kuma ce an sake shi ne a madadin wani jigon jam’iyyar tare da alkawarin cewa zai dawo ofishinsu don ci gaba da amsa tambayoyi a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin magauta ne saboda sun ga farin jinina na karuwa a jihar, Aliyu Sokoto

A halin da ake ciki, dan takarar gwamnan ya bayyana wadanda ke yada jita-jitan kamun nasa a matsayin yan siyasa, wadanda ke tsoron shaharar da ya yi.

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP mai adawa ce ta kitsa labarin karyan don bata masa suna, rahoton The Sun.

Sokoto ya jaddada cewar babu wani dalili da zai sa kowace hukuma ta yaki da cin hanci da rashawa ta gayyace shi ko kama shi, domin a cewarsa bai taba aikata wani aikin asshaa ba a lokacin da yake mulki wanda zai a gayyace shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Aliyu ya ce:

"Na yanke shawarar kin cewa komai tunda jita-jitan ya bayyana cewa an bukaci na dawo a ranar 14 ga watan Janairu ko a kama ni.
"A yau 14 ga watan Janairu, ina ta kaiwa da komowa a cikin garin Sokoto tun da safiyar yau ina ta tsammanin kamun wanda bai faru ba.
"A yanzu gani a nan garin Mabera da yammacin nan kuma na yanke shawarar fada masu cewa jita-jitansu ya kasance ne saboda shaharar da nake kara samu a tsakanin mutanen jihar."

Sai dai kuma, Aliyu ya shawarci yan siyasa da su daina siyasar kiyayya da dacin zuciya sannan sun habbaka manufofi.

Za mu bi duk wanda ya lashe zaben gwamna a Kano, Gawuna

A wani labarin, mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar APC a zaben gwamnan jihar na 2023, Nasiru Gawuna ya dauki alkawarin biyayya ga duk wanda Allah ya bai wa mulki a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng