Zaben 2023: Za Mu Bi Duk Wanda Allah Ya Nufa Da Zama Gwamnan Kano, Inji Gawuna

Zaben 2023: Za Mu Bi Duk Wanda Allah Ya Nufa Da Zama Gwamnan Kano, Inji Gawuna

  • Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, dan takarar APC a zaben gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna ya sha alwashin bin duk wanda Allah ya baiwa mulki
  • Gawuna wanda ya yi kira ga magoya bayan yan takara da su rungumi zaman lafiya, ya ce za su bayar da shawara mai kyau ga duk wanda ya zama gwamna don ci gaba jihar Kano
  • Sai dai kuma, mataimakin gwamnan mai ci ya yi kira ga al'ummar Kano da su duba cancanta yayin zabe

Kano - Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar All Progressive Congress (APC), Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa za su bi duk wanda Allah ya zama ya zama gwamnan jihar.

Gawuna wanda shine mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai ci a yanzu, ya kuma bayyana cewa za su ba duk wanda ya lashe zabe shawarwari domin ci gaban jiharsu, BBC Hausa ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Gindaya Wa Atiku, PDP Sharadi Na Karshe Gabanin Ranar Zabe

Gawuna
Zaben 2023: Za Mu Bi Duk Wanda Allah Ya Nufa Da Zama Gwamnan Kano, Inji Gawuna Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a yayin muhawara tsakanin masu neman kujerar shugabancin jihar Kano wanda sashin Hausa na BBC ya shirya a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu.

Gawuna ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

''Idan Allah ya nufa ya ba mu shugabanci za mu yi wa al'umma aiki; idan kuma Allah bai ba mu ba, za mu bi duk wanda ya ba kuma za mu ba shi shawara mai kyau domin ci gaban mutanen jahar Kano.”

Dan takarar ya kuma jaddada kira ga al'ummar jihar da su duba cancanta yayin zaben gwamna mai zuwa.

Ya kara da cewa:

“A duba cancanta yayin zaben dan takara."

Ya kuma yi kira ga yin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a domin a cewarsa ko da suka iso wajen muhawarar a daki daya aka sauke su shi da sauran abokan hamayyarsa kuma suna yi gaisuwa cike da mutuntawa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Kafa Sharadi 1 Da Zai Sa Ya Yi Wa Inyamurai Aiki Idan Zama Shugaban Kasa a 2023

Mambobin APC sama da 20,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Bauchi

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyar APC ta rasa dubban mambobinta a jihar Bauchi inda suka koma jam'iyyar PDP mai mulki a jihar.

Masu sauya shekar sun bayyana nasarorin da gwamnan jihar, Bala Mohammed ya samu musamman a fannin ababen more rayuwa a matsayin hujjarsu na komawa PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel