Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona

  • Wani sabon nauyin cutar Korona ya sake bulla kuma abin har ya shigo kasarmu nan Najeriya
  • Daya daga cikin masu neman zama shugaban kasar Najeriya bayan Buhari ya kamu da cutar
  • Ana fargabar wannan matsala na iya kawo tasku ga yakin neman zabe da ma zaben shi kansa

Abuja - Dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Dumebi Kachikwu, ya kamu da sabon nauyin cutar COVID-19 wacce akafi sani da Korona.

Kachikwu ya yi kira ga yan Najeriya su yi hattara saboda akwai yiwuwan cutar Korona ta sake dawowa yayinda ake shirin gudanar da zaben 2023 nan da wata guda.

Kachikwu ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Asabar a Abuja, rahoton Thisday.

Kachikwi
Da Yiwuwan A Daina Taron Kamfe, Babban Dan takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Sabuwar Nauyin Cutar Korona
Asali: Depositphotos

Ya ce tuni ya killace kansa kuma ya soke dukkan tarukan kamfen da ya shirya sai lokacin da ya barranta daga cutar.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A riwayar Vanguard, Ya yi kira ga yan Najeriya kada su yiwa lamarin yiwuwar dawowar Korona rikon sakainar kashi saboda a fadin duniya abubuwa sun fara kamari.

Yace:

"Wajibi ne yan Najeriya su yi hattara duk da cewa gwamnati ta sassauta dokokin COVID-19."
"Asibitocin ba zasu iya kwasan jama'a ba idan mutane da yawa suka kamu da cutar musamman yanzu da likitoci da malaman jinya ke guduwa daga kasar."
"Wajibi ne a kara kaimi wajen gwajin mutane saboda kada cutar ta yadu."
"Kada mu basri tarukan kamfe su zama hedkwatar yada cutar Korona saboda hakan koma baya zai zama ga nasarorin da aka samu a baya."

Ana wannan kuma ne lokacin da shugaba Buhari ke shirin kai ziyarar kamfe wasu jihohin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kai Ziyara Jihohi 8 Cikin Kwanaki 30

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kamu Da Cutar COVID19

Shugaba Buhari ya fara cika alkawarinsa na taya Asiwaju Bola Ahmed da jam'iyyar APC yakin neman zabe yayinda ake shiryawa zaben.

Kawo yanzu, Buhari yayi kamfe a jihohi biyu - Adamawa da Yobe - a makon da ya gabata.

Yanzu saura jihohi guda takwas cikin jerin jihohi goma shugaban kasan ya ce zai tafi yin kamfe.

Bullar wannan sabon nauyi na cutar Korona na iya kawowa wannan manufa ta yan siyasa babban cikas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel