Jam'iyyar PDP Ta Yi Babban Rashi Yayin Da Jigonta Da Magoya Bayansa Suka Koma APC

Jam'iyyar PDP Ta Yi Babban Rashi Yayin Da Jigonta Da Magoya Bayansa Suka Koma APC

  • Mr Goodluck Adenomo, jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da magoya bayansa sun koma, APC, All Progressives Congress, APC
  • Adenomo ya ce shi da magoya bayansa sun yanke shawarar komawa APC din ne don goyon bayan tazarcen Dennis Idahosa, mai wakiltar mazabar Ovia
  • Emma Ogbomo, shugaban jam'iyyar APC na Ovia South West ya yi maraba da wadanda suka sauya shekan ya ce za a musu adalci tamkar tsaffin yan jam'iyyar

Jihar Edo - Jigon jam'iyyar PDP na karamar hukumar Ovia ta Kudu a jihar Edo, Goodluck Adenomo, ya koma jam'iyyar APC tare magoya bayansa.

An tarbi Adenomo da sauran wadanda suka sauya shekar ne a hedkwatar APC a karamar hukumar, The Punch ta rahoto.

APC da PDP
Jam'iyyar PDP Ta Yi Babban Rashi Yayin Da Jigonta Da Magoya Bayansa Suka Koma APC. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyo ya fito, Atiku ya dawo daga Landan tare da wasu jiga-jigan PDP

Tsohon jigon na PDP, kamar yadda aka rahoto ya koma APC ne don yin aiki don tazarcen dan majalisa mai wakilta mazabar Ovia, Dennis Idahosa.

Adenowo ya jinjinawa dan majalisar yana mai cewa ayyukansa ya fi na sauran wadanda suka wakilci mazabar a baya.

Dalilin da yasa Adenomo ya koma jam'iyyar APC

Da ya ke jadada bukatar goyon bayan Idahosa, ya ce:

"Wannan dalilin shine yasa ni da magoya bayana muka yanke shawarar komawa APC don goyon bayan tazarcen Idahosa.
"Ayyukan da ya yi a ofis a cikin shekaru uku ya zama abin bude ida gare mu kan Ovia saboda sauran yan majalisa da suka zo a baya ba su yi irin aikinsa ba."

Ciyaman din APC a Ovia South West, Emma Ogbomo, wanda ya tarbi wadanda suka sauya shekan ya jinjinawa Adenowo yana cewa ya yi murna da zuwansa.

Ya ce:

"Mun yi murna da zuwan ka kuma muna son ka sani za ka samu dukkan alfarma da ake yi wa tsaffin mambobi."

Kara karanta wannan

2023: Shaharraren Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Zai Faru A Zaben Gwamnan Katsina, Abia Da Taraba

Yar Takarar Kujerar Mataimakin Gwamna Ta Fita Daga APC Ta Koma PDP

Helen Boco, tsohuwar yar takarar kujerar mataimakiyar gwamnan a zaben shekarar 2019 a jihar Cross Rivers a APC ta koma jam'iyyar PDP.

A cewar wani rahoto da Trinune Online ta wallafa, Boco ta sauya shekar ne yayin da ya rage kwana 49 a yi babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Ta yi korafin cewa duk da muhimmin gudunmawa da ta bada wurin gina jam'iyyar APC, shugabannin jam'iyyar sun mayar da ita saniyar ware.

Asali: Legit.ng

Online view pixel