Jam’iyyar NNPP Ta Fasa Kwai, Wanda Aka ba Takara Ya Yaudare ta Bayan Karbar N500m
- Shugaban jam’iyyar NNPP ya ce sun yi nasara da suka je kotu domin su canza wasu ‘yan takaransu
- Farfesa Ahmed Rufai Alkali ya ce sun canza ‘dan takaran mataimakin Gwamnan da ya saida tikitinsa
- NNPP ta cire sunan Ibrahim Shekarau da wasu ‘yan takaran da suka sauya-sheka da lokaci ya kure
Abuja - Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Ahmed Rufai Alkali ya zargi ‘dan takaransu na mataimakin Gwamna a jihar Yobe da cin amana.
The Nation ta rahoto Farfesa Ahmed Rufai Alkali ya ce wani wanda jam’iyyar NNPP ta ba takara ya saida tikitinsa, ya yi watsi da zaben da za a shiga.
Da yake yi wa manema labarai bayani a garin Abuja a kan dalilinsu na shigar da karar hukumar INEC, ya zargi wanda aka ba takara da cin amana.
Ganin hukumar zabe ta ki bada dama, jam’iyyar adawa ta NNPP ta ke kotu domin ta iya canza wasu daga cikin ‘yan takaranta da suka canza sheka.
Za a shiga zabe babu mataimakin Gwamna?
Farfesa Alkali bai kama suna ba, amma ya ce wanda suka ba tikitin takarar mataimakin gwamnan Yobe ya karbi N500m, ya yi watsi da zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
The Cable ta rahoto shugaban jam’iyyar mai alaman kayan marmari yana cewa kotun tarayya ta umarci INEC ta amince da sababbin ‘yan takaransu.
Alkali ya ba NNPP gaskiya a Kotu
Alkali ya yabi hukuncin da Alkalan kotun tarayya da na kotun daukaka kara suka yi, yake cewa jam’iyyar NNPP ta amfana da adalcin wadannan kotu.
A jawabin da ya yi a ranar Larabar, shugaban NNPP na kasa ya yabi hukumar INEC a karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu wajen bin doka.
A cewar Farfesan, kotun tarayya ta amince da bukatar NNPP na canza sunan ‘yan takaran majalisar tarayya kusan 80 da aka gabatar a karon farko.
Alkali ya ce duk da hukumar INEC ta na da ka’idojinta, amma dokar zabe ta na gaba da ita idan ana maganar wa’adin gabatar da sunan masu yin takara.
Legit.ng Hausa ta fahimci NNPP ta canza Ibrahim Shekarau da John Ikenya da suka fice daga jam’iyyar zuwa PDP da LP bayan sun samu takarar Sanata.
APC ta karfafa shirin zabe
An ji labari Bola Tinubu, Kashim Shettima, Adams Oshiomhole, Hadiza Bala Usman da James Faleke sun yi kwana biyu a jere ana taro kan shirin takara.
Abubakar Bagudu, Badaru Abubakar, Nasir El-Rufai, Inuwa Yahaya, Yahaya Bello, Bello Matawalle da wasu Gwamnonin sun halarci zaman da aka yi.
Asali: Legit.ng