Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Yayin da Tinubu Ya Ziyarci Gwamnan G5, Ifeanyi Ugwuanyi

Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Yayin da Tinubu Ya Ziyarci Gwamnan G5, Ifeanyi Ugwuanyi

  • Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya gaba da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu a fadar gwamnatin jihar
  • Tinubu wanda ya samu rakiyar Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da Hope Uzodinma na jihar Imo ya gaba da gwamnan bayan gangamin kamfen dinsa a jihar
  • A baya an ce dan takarar shugaban kasar na APC ya kulla yarjejeniya da gwamnonin G5 a Landan, inda duk suka karyata

Enugu - Ana kara samun tashin hankali a sansanin Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP yayin da takwaransa na APC, Bola Tinubu, ya gana da daya daga cikin fusatattun gwamnonin jam’iyyarsa.

Biyo bayan kamfen dinsa a Enugu a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu, Tinubu ya kai ziyarar bangirma ga Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi a fadar gwamnatin jihar, lamarin da ba a saba gani ba tattare da dan takarar shugaban kasar na APC.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin G5 Sun Goyi Bayan Atiku A Sirrance? Sabbin Bayanai Sun Bayyana

Tinubu ya ziyarci Ifeanyi Ugwuanyi
Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Yayin da Tinubu Ya Ziyarci Gwamnan G5, Ifeanyi Ugwuanyi Hoto: Tinubu/Shettima Media Support
Asali: Twitter

Tinubu ya hadu da na hannun daman Wike a Enugu

Ungwuanyi na daya daga cikin fusatattun gwamnonin PDP da ake kira da G5 ko ‘Integrity Group’ kuma sun sha alwashin cewa ba za su tsoma baki a kamfen din shugaban kasa na Atiku ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran gwamnonin G5 sun hada da Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abia, Seyi Makinde na Jihar Oyo da Samuel Ortom na jihar Benue.

A kwanaki ne aka rahoto cewa Tinubu ya kulla yarjejeniya da gwamnoni 4 cikin 5 na PDP a Landan amma tsohon gwamnan na jihar Lagas ya karyata kulla yarjejeniya da G5 da Wike ke jagoranta.

Jam’iyyar PDP a daya bangaren ta sha alwashin dakatar da gwamnonin G5 da kuma rushe tsarin jam’iyyar a jihohinsu idan suka ayyana goyon bayansu ga wani dan takara ba Atiku ba.

Kara karanta wannan

An ramawa Atiku: Gwamna mai ci da 'yan takarar gwamna 2 sun ki halartar kamfen PDP

Gwamnonin na sun karyata batun kulla yarjejeniya da kowani dan takara kuma cewa za su bayyanawa magoya bayansu dan takarar da suke goyon baya.

Kalli hotuna da bidiyon:

Kungiyar CAN ta shawarci matasa da su zabi san ransu ba tare da la'akari da addini ba

A wani labari na daban, kungiyar kiristocin Najeriya ta shawarci matasa a kan kada su yarda su saida yancinsu da kuri'unsu a babban zaben wata mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng