Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar da Ya Nemi Tikitin Gwamna a Zamfara

Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar da Ya Nemi Tikitin Gwamna a Zamfara

  • Jam'iyar PDP mai adawa ta fatattaki dan takarar da ya nemi tikitin gwamna a jihar Zamfara, Ibrahim Shehu Bakauye
  • A wata takarda da jam'iyyar ta aike masa a gundumar Mayana, Gusau tace ta yi nazari kan ayyukan cin amanar da yake yi ta bayan fage
  • Bayan rashin nasara a zaben fidda dan takara, Shehu Bakauye ya garzaya Kotu ya nemi a soke sakamakon zaben PDP

Zamfara - Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara ta kori Honorabul Ibrahim Shehu Bakauye, dan takarar da ya nemi tikitin gwamna a jam'iyar kan zargin cin amana.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Bakauye tare da sauran yan takara sun fafata a zaben fidda dan takarar gwamnan Zamfara na jam'iyyar PDP wanda ya gudana a 2022.

Shehu Ibrahim Bakauye.
Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar da Ya Nemi Tikitin Gwamna a Zamfara Hoto: leadership
Asali: UGC

Bayan shan kaye hannun Dauda Lawal a zaben fidda gwanin na ranar 25 ga watan Mayu, 2022, Hon. Bakauye ya garzaya Kotu ya roki a rushe sakamakon zaben.

Kara karanta wannan

2023: Shahararrun Mawakan APC a Arewacin Najeriya G-11 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

A wasikar korar tsohon dan takarar, mambobin kwamitin zartaswa na PDP a mazabarsa gundumar Mayana, karamar hukumar Gusau sun zauna sun yi nazari kan ayyukan Bakauye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wasikar, PDP ta zargi Bakauye da rashin da'a da kuma bi ta bayan fage wajen hada kai da jam'iyyar APC mai mulki a rushe jam'iyar adawa.

Wani sashin wasikar korar da PDP ta aike wa dan takara ya ce:

"Bayan zaben fidda gwani wanda ka nemi zama dan takarar gwamnan Zamfara a babban zabe mai zuwa karkashin inuwar PDP da kuma zagon kasan da ka koma yi wa jam'iyya da mambobinta a gunduma, karamar hukuma da jiha."
"Kwamitin gudanarwa na Mayana, Gusau, Zamfara ya gano ka aikata abubuwa da suka hada da daukar matakin yakar jam'iyya ta hanyar shigar da kara Kotu wanda ya saba wa sashi na 58 (1) L na kundin dokokin PDP."

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe: Alkali ya sa a kamo masa dan takarar gwamnan PDP a wata jiha

"Haka nan ka sa hannu a ayyukan cin amana da zagon kasa wanda ya saba wa sashi na 58 (f) (h) da (i), da kuma rashin da'a da ya saba wa 58 (l) (a) (b) (c) na kwansutushin din PDP da aka yi wa garambawul 2017."

Bayan gama jero laifukan da ake zargin dan siyasan da aikata wa, PDP ta sanar da cewa ta kori Bakauye daga inuwar jam'iyyar kuma matakin zai fara ne daga watan Janairu.

A ruwayar Vanguard, sanarwan ta cigaba da cewa:

"Duba da haka, Hon. Ibrahim Shehu (Bakauye) Gusau, tsohon mamban PDP a Gundumar Mayana, mun kore ka daga jam'iyya kuma mun soke katin zama mambanka daga watan Janairu, 2023."

Atiku Abubakar Ya Tafi Hutawa Ne Amma Lafiyarsa Kalau, Hadimi Ya Yi Karin Haske

A wani labarin kuma Makusantan Atiku sun bayyana dalilin daina jin duriyar dan takarar shugaban kasan a baya-bayan nan

Kara karanta wannan

Abuja: Buhari ya Gana da Aisha Binani a Fadarsa Tara da Wasu Jiga-jigan APC

A 'yan kwanakin ana ta kace-nace a kafafen sada zumunta kan ina Atiku Abubakar ya shiga aka daina jin duriyarsa.

Daraktan kwamitin sadarwa da zabe na tawagar kamfen PDP , Chief Dele Momodu, ya roki 'yan Najeriya su shure rahoton dake zargin Atiku na fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel