Fitattun Mawakan APC G11 a Arewacin Najeriya Sun Koma Jam'iyar PDP

Fitattun Mawakan APC G11 a Arewacin Najeriya Sun Koma Jam'iyar PDP

  • Kwanaki kasa 50 gabanin zaben shugaban kasa a watan Fabrairu, jam'iyyar APC ta yi babban rashi a jihar Bauchi
  • Mashahuran mawakan G-11 da suka shafe kusan shekara 10 tare da APC sun sauya sheka zuwa PDP mai mulkin jihar
  • Jagoran mawakan, Andy Bature, yace zasu zama masu biyayya ga PDP don tabbatar da nasarar yan takararta a 2023

Bauchi - Gabanin babban zaben watan Fabrairu mai zuwa, mashahurin mawakin nan na Bauchi, Andy Bature, ga jagorancin tawagar G-11 ta mawakan APC sun sauya sheka zuwa PDP.

Andy da sauran fitattun mawakan da ake kira G-11 sun daɗe suna wa jam'iyar APC aiki kusan shekaru 10 kuma sun rera wakokin da suka karbu ga yan takarar APC a Bauchi da kasa baki daya.

Manyan jam'iyyu biyu.
Fitattun Mawakan APC G11 a Arewacin Najeriya Sun Koma Jam'iyar PDP Hoto: leadership

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yayin da yake jawabi a ofishin kamfen dan takarar gwamna na PDP, inda aka musu maraba, Andy ya bayyana dalilansu na barin APC.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Dauki Babban Alkawari a Gaban Buhari a Yola, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

Mawakin ya ce sun yanke tattara kayansu daga APC ne sabida rashin maida hankali da kuma girmama bukatun mambobi a tsohuwar jam'iyar da suka baro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma kara da cewa zasu zama masu biyayya ga tsarin jam'iyar PDP ta Bauchi kuma su ba da gudummuwa wajen nasarar yan takararta a zabe mai zuwa.

Mista Andy ya ce tawagar mawakan siyasa G-11 na goyon bayan kudirin tazarcen gwamna Bala Muhammad bisa la'akari da dumbin ayyukan alheri na ci gaba da ya zuba wa mutane a zangon farko.

PDP zata dora daga inda fa tsaya

Da yake maraba da G-11, mataimakin darakta Janar na kwamitin ayyuka a tawagar kamfen PDP, Abdulrazak Nuhu Zaki, yace gwamnatin Kauran Bauchi zata dora daga inda ta tsaya.

Yace gwamnatin Bauchi zata ci gaba da jawo kowa a jiki a kokarinta na samar da walwala da jin dadi ga talakawan Bauchi ba tare da nuna banbanci ko bangaranci ba.

Kara karanta wannan

Adamawa Ta Cika Ta Batse Yayin da Shugaba Buhari Ya isa Mahaifar Atiku Don Yakin Neman Zaben APC

A cewarsa nasarorin da gwamna ya cimma ya samo tushe ne daga goyon baya da Addu'ar da mutane ke mata, inda ya kara da cewa akwai fiye da haka idan ta zarce zango na biyu.

NNPP ta kaddamar da kwamitin kamfe a Abuja

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso Ya Bayyana Kwamitin Yakin Neman Zaben NNPP 2023

Bayan dogon lokaci, Kwankwaso ya kaddamar da mambobin tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na NNPP mai kayan dadi a Abuja yau.

"Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, ina mai kaddamar da kwamitin neman gina sabuwar Najeriya daga 29 ga watan Mayu" inji Kwnakwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel