Rikicin PDP: A Karshe Atiku da Jam'iyya Sun Sauko, Sun Roki Wike da Sauran Gwamnonin G-5
- Ga dukkan alamu rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP na gab da zuwa karshe
- Gabannin babban zaben wata mai zuwa, shugabancin PDP ya yi kira ga Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da mukarrabansa da su hada hannu su yi aiki don ci gaban jam’iyyar
- Wannan rokon na zuwa ne bayan magoya bayan Atiku Abubakar sun nunawa dan takarar na PDP cewa suna tare da shi a lokacin kamfen din Makinde a Ibadan
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamnonin G-5 da su hada hannu da jam’iyyar don cimma kudirinta na kwatowa da sake gina Najeriya.
Da yake martani ga ihun “Atiku, Atiku, Atiku” da wasu suka yi a Ibadan yayin kaddamar da yakin neman zaben Gwamna Oluseyi Makinde, kakakin PDP, Charles Aniagwu, ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da rokon gwamnonin G-5 kan su ajiye makamin yakinsu sannan su dawo inuwar jam’iyyar.
PDP ta roki Wike da mukarrabansa, ta fadi dalili
Sai dai kuma, ya ce karfin ikon zabar shugabanni na a hannun mutane ne kuma wani jagora bai da hurumin yanke hukunci, yana mai cewa zamanin da ake juya masu zabe ya wuce domin mutane ne ke da yancin yin haka, rahoton Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce martanin yawancin mutane a gangamin kamfen din Ibadan ya nuna cewa tikitin Atiku Abubakar da abokin takararsa, Dr Ifeanyi Okowa sune mafi soyuwa don ceto Najeriya daga barnar gwamnatin APC.
Aniagwu ya ce:
“Mun sha fadin cewa jirginmu ya bar tasha amma saboda muna da birki mai ci da kyau Muna iya tsayawa a koina don daukar fasinjoji.
“Saboda haka za mu ci gaba da rokon shugabanninmu, gwamnonin G-5 da su ajiye makaman yakinsu sannan su dawo inuwar jam’iyyar da hada hannu wajen cimma kudirin jam’iyyar na cetowa da sake gina Najeriya.”
Atiku ne zai iya biyan bashin tiriliyan 77 da ake bin Najeriya, matasan PDP
A wani labari na daban, wata kungiya ta matasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP sun ce Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa da zai iya raba Najeriya da tulin bashin naira tiriliyan 77 da ake bin ta.
Asali: Legit.ng