Atiku Ne Dan Takarar Da Zai Iya Daidaita Bashin Triliyan N77 da Ake Bin Najeriya, Inji Matasan PDP

Atiku Ne Dan Takarar Da Zai Iya Daidaita Bashin Triliyan N77 da Ake Bin Najeriya, Inji Matasan PDP

  • Shugaban Najeriya mai zuwa a 2023 zai gaji bashin naira tiriliyan 77 daga gwamnatin Buhari
  • Ofishin kula da bashi na kasa ne ya bayyana a kwanan nan cewa gaba daya bashin da ake bin gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha da na Abuja ya kai triliyan N44.06
  • Hakan na nufin cewa yawan kudin zai tashi zuwa naira triliyan 77 a lokacin da gwamnatin Buhari za ta sauka daga mulki

Abuja - Wata kungiya karkashin inuwar People’s Democratic Party (PDP) mai suna PDP New Generation ta bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar, shi ya fi cancanta ya ja ragamar bashin naira tiriliyan 77 da ake bin Najeriya a yanzu.

Kungiyar na martani ne ga rahoton ofishin kula da hada-hadar bashi na kasa da ke cewa magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gaji a kalla bashin naira tiriliyan 77.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Audu Mahmood
Atiku Ne Dan Takarar Da Zai Iya Daidaita Bashin Triliyan N77 da Ake Bin Najeriya, Inji PDP New Generation Hoto: @pdpnewgen
Asali: Twitter

Jawabin wanda ke dauke da sa hannun darakta janar na kungiyar, Audu Mahmood kuma ya aikawa Legit.ng ya bayyana cewa rahoton DMO ya nuna cewa Najeriya na gab da shiga tarkon bashi.

Jawabinsa na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Lokacin da gwamnatin PDP ta bar mulki a 2015, ta bar bashin naira tiriliyan 15. Buhari zai bar mulki a 2023 da bashin da ya kai tiriliyan 77.
“Babu makawa gwamnatin shugaba Buhari mai barin gado annoba ce. Ya zama dole yan Najeriya su tabbatar da ganin cewa basu sake zabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), don kasar ta shiga tarkon bashi.
“Najeriya na hanyar rugujewa, mun tsunduma tsundum a cikin bashi kuma gwamnatin APC rudu ce. Wannan zaben ne ya yiwa yan Najeriya saura su kare kansu.
“Najeriya ta yi amfani da kimanin 80.6% na kudaden shigarta kan bashi a 2022. Kuma a haka, suna neman sabon bashi na tiriliyan 8.8. Yanzu ya tabbata cewa APC na son ruguza Najeriya ne.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Shugaba Buhari Ya Fada Wa Mutanen Adamawa Game da Zaben Mace Ta Zama Gwamna

“Yana da muhimmanci kasar ta zabi Atiku Abubakar don kare kasar nan daga tabarbarewa.”

Mahmood ya ci gaba da cewa Atiku ya fi fahimtar tattalin arzikin Najeriya saboda gogewarsa yana mai cewa sauran yan takarar abu kadan suka fahimta game da shugabanci.

Ya Kara da cewar yan Najeriya na bukatar Atiku don ya ceto su a lokaci irin wannan.

Magajin Buhari zai sha bashi

Da farko Legit.ng ta rahoto cewa Ofishin da ke kula da hada-hadar bashi na kasa ya bayyanawa yan Nigeria bashin da ake bin kasar ya kai naira tiriiyan 77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel