Mata Sun Cancanci Zama Shugabanni, Ku Zabi Binani, Buhari Ga Mutanen Adamawa

Mata Sun Cancanci Zama Shugabanni, Ku Zabi Binani, Buhari Ga Mutanen Adamawa

  • Shugaba Buhari yace idan aka zabi Sanata Aishatu Binani a jihar Adamawa mata zasu samu kwarin guiwar shugabanci
  • Buhari yace idan ta zama gwamna mace ta farko a Najeriya, duniya zata fahinci wayewar siyasa da shugabancin kasar nan
  • Gwamna Ahmadu Finfiri ya gode wa shugaban kasa bisa taimakon da ya yi wa Adamawa a mulkinsa

Adamawa - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ranar Litinin a Yola, yace zaben Sanata Aishatu Ahmed Binani a matsayin gwamnan Adamawa ta gaba zai bude kofofin damarmaki ga mata a faɗin kasar nan.

Channels tv ta tattaro Buhari na cewa idan har mace ta zama gwamna zata aika alamar wayewar siyasa a Najeriya ga sauran kasashen duniya.

Shugaba Buhari a Adamawa.
Mata Sun Cancanci Zama Shugabanni, Ku Zabi Binani, Buhari Ga Mutanen Adamawa Hoto: @buharisallau
Asali: Twitter

Da yake jawabi a fadar Lamidon Adamawa, shugaban ƙasan yace yana goyon bayan yar takarar gwamnan APC da sauran 'yan takarar jam'iyyar kuma zai ci gaba da basu goyon bayan da ya kamata domin su yi nasara a zabe.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Shin Dagaske An Garzaya da Atiku Abubakar Asibiti Neman Lafiya? Gaskiya Ta Bayyana

A kalamansa, Buhari ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na zo nan ne domin na tabbatar da cewa tun daga karshen Najeriya zuwa sauran sassa, ina tare da yan takarar mu, Sanata Binani, da sauran 'yan takara."
"Mun zo nan mu tabbatar Sanata Aishatu Binani ta zama zababbiyar gwamna mace ta farko da izinin Allah. Zabenta kadai ya isa bayani ga Najeriya da duniya ta jihar Jihar Adamawa."
"Ina kara gode muku sosai bisa goyon bayan da kuka bani kuma ina son dukkan ku ku mara mata baya ta samu nasara. Haka kuma ga masu neman takara a tsagin Adawa ina muku fatan Alheri."

Ya kamata mata su shigo a dama da su - Buhari

Buhari ya kara da cewa mata sun jima suna fafutuka daga nesa ya kamata su matso kusa a dama da su a shugabanci.

Kara karanta wannan

Adamawa Ta Cika Ta Batse Yayin da Shugaba Buhari Ya isa Mahaifar Atiku Don Yakin Neman Zaben APC

"Zamu goya mata baya da halayen mu na kirki, mata sun jima suna fafutuka daga nesa, ya kamata su matso kusa a halin yanzu kuma a raba shugabanci tare da su."

A nasa jawabin, gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya gode wa shugaban kasa Buhari bisa taimaka wa jihar ta bangarori da dama.

Punch ta rahoto gwamnan na cewa:

"Ina amfani da wannan dama na maka barka da zuwa gidanka na biyu. Muna kara gode maka bisa manyan ayyukan da ka aiwatar a Adamawa, duk wata bukata da muka kai maka ka biya mana."

APC ta sake rasa jiga-jigai a Bauchi

A wani labarin kuma Shahararrun Mawakan APC a Arewacin Najeriya G-11 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Mashahuran mawakan APC da ake wa lakabi da G-11 a jihar Bauchi sun jingine tafiyar Tinubu, sun koma jam'iyyar PDP.

Kafin yanzu, Mawakan sun rera daɗaɗan wakoki ga dan takarar shugaban kasa na na gwamna Bauchi a inuwar APC kusan shekaru 10.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel