Na Kusa da Tinubu Ya Bada Somin-Tabin Lakanin da Za Ayi Amfani da Shi a Ci Zabe

Na Kusa da Tinubu Ya Bada Somin-Tabin Lakanin da Za Ayi Amfani da Shi a Ci Zabe

  • Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji ya fara bayanin irin yadda jam’iyyar APC za ta bi wajen cin zaben bana
  • Sanusi Rikiji ya nuna APC za ta shawo kan masu sana’o’in hannu su zabi Bola Tinubu a yankin Arewa
  • Kuri’u sama da miliyan 5 jam’iyyar APC mai mulki take nema daga wajen masu yin sana’o’in hannu

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Zamfara, Sanusi Garba Rikiji yana ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai bada mamaki a zaben bana.

A wani rahoto da The Nation ta fitar, an ji Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji yana cewa ba za a sanar da jama’a lakanin APC ba sai bayan sun lashe zabe a Fubrairu.

Sanusi Rikiji shi ne shugaban sashen masu sana’ar hannu da gyare-gyare a Arewa maso yammacin na kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

"Gwamnoni 11 da Sanatocin Jam’iyyar APC 35 Suna Yi wa Atiku Aiki a Boye a Arewa"

Tsohon ‘dan majalisar dokokin ya ce kuri’u kimanin miliyan 5.3 suke hari daga wajen masu kananan sana’o’in hannu da ake da su a jihohin Arewa ta yamma.

APC tana neman wadannan kuri’u daga masu sana’o’in hannu miliyan 7.5 da suka yi rajista da CAC.

Jawabin Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji

Me nake fada, ta ya za mu cin ma wannan nasara? Mun fito da dabaran da muke sa ran zai kai mu ga nasara, tsari ne na aikin 30-30 a yankunan kasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu
Yakin neman zaben APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

‘Yan jarida ba za su san abin da muke nufi da 30-30 ba, mu na kamfe saboda haka ba za mu fitar da sirrin ba, muna tabbatar maku za mu shiga ko ina.
Tsarinmu na 30-30 zai shiga kowane lungu da sako na kananan hukumomi 774 da ke kasar nan, samun kuri’u miliyan 5.3 daga Arewa ba zai gagara ba.

Kara karanta wannan

Atiku Zai Tashi a Tutar Babu, Gwamnan Arewa Ya yi wa APC Alkawarin 99.9% na Kuri’unsa

A hirar da aka yi da shi, Rikiji ya godewa shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa da suke goyon bayan takararsu, musamman kokarin da suka yi a Kano.

Alakar Rikiji da Femi Gbajabiamila

Baya ga haka, ‘dan siyasar yana neman kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Gusau/Tsafe a APC bayan ya yi aiki da Hon. Femi Gbajabiamila.

Tun 2019, Rikiji ya kasance shugaban ma’aikatan ofishin shugaban majalisar wakilan tarayya, wanda yana cikin ‘yan siyasar da Bola Tinubu ne ya fito da su.

Mu na tare da Obi, LP -NLC

A wani rahoto mai kama da wannan, an ji labari babu ruwan kungiyar kwadago ta kasa da Atiku Abubakar ko Bola Tinubu a zaben shugabancin Najeriya.

Shugaban NLC a Najeriya, Kwamred Ayuba Wabba ya ce za su zabi Peter Obi da duk wanda aka ba takarar kujera a LP domin ita ce jam’iyyar 'yan kwadago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng