Ku Yi Watsi da Farfaganda, Peter Obi Ya Kafu a Arewa, Inji Kakakin Labour Party

Ku Yi Watsi da Farfaganda, Peter Obi Ya Kafu a Arewa, Inji Kakakin Labour Party

  • Jam'iyyar Labour Party ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa bata da wakilan zabe a fadin rumfunar zabe 90,000 da ke yankin arewacin Najeriya
  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na LP, ya jaddada cewa Peter Obi ya kafu sosai a arewa kuma zai ba da mamaki a zabe mai zuwa
  • Kakakin kwamitin, Dr Yunusa Tanko, ya ce za su gudanar da bincike don gano daga inda farfagandan ya fito

Kakakin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar Labour Party (LP), Dr Yunusa Tanko, ya shawarci yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin da jam'iyyar adawa ke yi cewa basu da wakilan zabe a jihohin arewa.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, Tanko ya bayyana cewa LP ta kafu kuma ita ce kan gaba kuma za ta kawo sauyi a zaben 2023, jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai Uku da Zasu Ja Hankalin 'Yan Arewa Su Zabi APC a 2023, Gwamna

Peter Obi
Ku Yi Watsi da Farfaganda, Peter Obi Ya Kafu a Arewa, Inji Kakakin Labour Party Hoto: Thisday
Asali: UGC

Channels TV ta nakalto Tanko yana cewa:

"Kokarin abokan hamayya na sanyaya gwiwowin yan Najeriya na zabar Peter Obi da Datti Baba-Ahmed a shekarar nan ba zai cimma nasara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An ja hankalin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party zuwa ga wani bayanin yaudara da ke yawo a kafofin soshiyal midiya cewa jam'iyyarmu bata gabatar da sunayen wakilai na rumfunar zabe 90,000 da ke arewa ta tsakiya, arewa da gabas da arewa ta yamma ba.
"Muna kallon hakan a matsayin wani farfaganda daga abokan hamayya don ruguzo da sunan da muka yi da kuma yaudarar masu zabe a shekarar zabe.
"Muna da wakilai a gaba daya kasar wadanda ma sun fi yawan adadin wakilan da ake bukata a kowace rumfar zabe. Don haka, batun rashin tura sunayen wakilai na mazabu 90,000 kanzon kurege ne daga makiyan ci gaba a Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

Ku yi watsi da batun sannan ku karbi katunan zabenku, LP ga magoya bayanta

Kwamitin ya kuma ce yana nan yana gudanar da bincike don gano tushen wannan farfaganda domin a cewarsa ba daga hukumar INEC batun ya fito ba.

Sun kuma yi kira ga magoya bayan jam'iyyar da su yi watsi da batun sannan su mayar da hankali wajen karbar katunan zabensu don fatattakar makiyan Najeriya.

Atiku ne zai iya raba Najeriya da bashin da ake bin ta

A wani labari na daban, wata kungiyar matasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ta bayyana cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP shi kadai ne zai iya raba Najeriya da bashin naira tiriliyan 77 da gwamnatin Buhari za ta bari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng