Zaben 2023: Abun da Yasa Na Janye Daga Takarar Dan Majalisa — Alan Waka

Zaben 2023: Abun da Yasa Na Janye Daga Takarar Dan Majalisa — Alan Waka

  • Gabannin zaben 2023, mawakin Kannywood, Aminu Ladan Abubakar, ya janye daga takarar kujerar majalisar wakilai
  • Mawakin wanda aka fi sani da Alan Waka ya ce ya janye ne domin kada ya take dokar kasa da ta hukumar zabe
  • Ya ce tsawon lokacin da ya dauka yana kiran kansa da dan takara a zabe mai zuwa, ba shi da wata shaida da ke nuni tare da tabbatar da hakan

Kano - Shahararren mawakin nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan Waka ya janye daga tseren kujerar Majalisar Wakilai.

Alan Wakan dai na neman takarar dan majalisa mai wakiltar karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano a majalisar dokokin tarayya.

Aminu Ala
Zaben 2023: Abun da Yasa Na Janye Daga Takarar Dan Majalisa — Alan Waka Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rahoto, mawakin ya bayyana cewa a baki ne kawai yake sunan dan takara domin bashi da wata takarda da ke nuna cewa lallai shi din dan takara ne.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

Aminu Ala ya ce ba shi da wata kwakkwarar shaida cewa shi dan takara ne a jam'iyyar da yake takara har zuwa yanzu da zabe ya saura kwanaki 55 zuwa 56.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta nakalto Ala yana cewa:

“Na sha sanar da jama'a cewa ni din dan takara ne. Amma fa kamar yadda nake fada, ni ma haka ji kawai nake yi saboda ba ni da wata takarda da nake nuni ga hakan.
"A yau da nake magana zabe ya saura kwanaki 55 ko 56, amma ba ni da wata shaida da ke nuna cewa ni din dan takara ne a jam’iyyar da nake takara. Jama’a Najeriya akwai doka.
"A daidai wannan ga'bar, duba da alkawarin da muka yi da Jam’iyyar ADP cewa in muka shiga jam’iyyar za a ba mu takara a karkashin kungiyar 13X13.

Kara karanta wannan

Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin da Karamar Diyarsa Ta Yi Alkawarin Siya Masa Mota, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

"Sai dai kuma, tun bayan da aka yi wannan batu, ita kanta kungiyar ban ga wani motsi da ta yi ba na ’ya’yanta na takara.
"Magana kawai muke yi daga wadanda ba su da hurumi. Abin da nake nufi shi ne jam’iyya ce kadai ke da hurumin mika dan takararta ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.
"Har yanzu ba mu samu wannan alama ko daya ba. Kuma alamomi sun nuna lallai lokaci ya kure mana.
"Bisa ga wannan dalili kuma don kada na taka dokar kasa, hukumar zabe da ta jam’iyya ne ya sa na rubuta takardar ficewa daga jam’iyyar, kuma ba na cikin ’yan takarar na karamar Hukumar Nasarawa.”

Ba za mu kwancewa juna zani a kasuwa ba idan muka lashe zabe - Tinubu ya yi shagube ga Atiku da Obasanjo

A wani labarin, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce za su ci gaba da mutunci da abokin takararsa, Kashim Shettima idan suka lashe zabe a 2023.

Tinubu ya sha alwashin cewa ba za su dunga kwancewa juna zani a kasuwa kamar yadda Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar suka yi ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel