Yan Takarar Majalisa Guda Shida Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Arewa

Yan Takarar Majalisa Guda Shida Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Arewa

  • Yan takarar majalisar dokoki a inuwar Labour Party Takwas sun sauya sheka zuwa jam'iyar APC a jihar Jigawa
  • Gwamna Muhammad Badaru ne ya karbe su a wani dan taro na musamman da aka shirya a gidan gwamnatin Jigawa ranar Jumu'a
  • Manyan 'yan siyasan sun ce sun yanke shiga APC ne bayan hango gobe mai kyau a jikin jam'iyyar

Jigawa - Takwas daga cikin masu neman zama mambobi a majalisar dokokin jihar Jigawa a inuwar Labour Party sun sauya sheka zuwa jam'iyar All Progressive Congress (APC) ranar Jumu'a 6 ga watan Janairu, 2023.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa 'yan takarar sun fito ne daga mazabun Auyo, Kirikasamma, Bulangu, Malam Madori, Kafin Hausa, Birniwa, Guri da Kaugama a jihar Jigawa.

Sauya sheka a Jigawa.
Yan Takarar Majalisa Guda Shida Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Arewa Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

'Yan siyasan sun samu kyakkyawar tarba daga gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa a wani kwaryakwaryan taro da aka shirya a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Tinubu zai tashi a tutar babu: Dan takarar gwamna a Arewa ya bar APC, ya shige inuwar PDP

Mai taimaka wa gwamna Badaru ta bangaren midiya, Habibu Kila, shi ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Kila ya kara da cewa ba ya ga yan takarar majalisa, gwamna Badaru ya kuma tarbi mamban kwamitim kamfen Peter Obi na LP, wanda ya sauya sheka zuwa APC.

Sanarwan ta ce:

"Gwamna Badaru ya yaba wa masu sauya shekar kuma ya masu alkawarin za'a tafi tare da su a harkokin jam'iyya kana ya roke su da su zama mambobi masu biyayya."

Meyasa suka sauya sheka daga LP zuwa APC?

Daya daga cikin jiga-jigan da suka bar Labour Party, Muhammad Makinta, daga karamar hukumar Guri, wanda ya yi jawabi a madadin saura, yace sun yanke shiga APC ne bayan gano ita ta dace da inganta rayuwar talakawa.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

Makinta ya bayyana cewa zasu yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar baki daya 'yan takarar jam'iyar APC a babban zabe mai zuwa tun daga har sama.

Da yake masu maraba zuwa jam'iyya mai mulki, shugaban APC na Jigawa, Aminu Gumel, ya tabbatarwa sabbin mambobin cewa za'a basu duk wata dama da hakki da kowane mamba ke samu.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Magantu Kan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Marawa Baya a Zaben 2023

Ga dukkan alamu gwamna Nyesom Wike, jagoran G-5 ya yanke cewa ba zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ba a zabe mai zuwa.

An ji gwamnan na cewa duk zagin da za'a masa da tsangwama ba zai ya sauya kudirinsa na yi wa dan takarar da yake so aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel