Yan Takarar Majalisa 8 Na Jam'iyyar Peter Obi Sun Koma APC A Shaharariyar Jihar Arewa

Yan Takarar Majalisa 8 Na Jam'iyyar Peter Obi Sun Koma APC A Shaharariyar Jihar Arewa

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Jigawa ta samu babban karuwa a yayin da yan takarar majalisar dokokin jiha karkashin jam'iyyar LP suka shigo APC
  • Gwamnan Muhammadu Badaru Abubakar na Jigawa ne ya tarbi wadanda suka sauya shekan a wani taro da aka yi a gidan gwamnati a Dutse, babban birnin jihar
  • Tsaffin yan takarar na jam'iyyar Labour sun ce sun dauki wannan mataki ne bayan ganowa cewa APC ce jam'iyya mafi nagarta a kasar, kuma sunyi alkawarin aiki don ganin ta yi nasara

Jihar Jigawa - Yan takarar majalisar dokokin jiha na jam'iyyar Labour su takwas a Jigawa sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, APC, The Cable ta rahoto.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, Habibu Nuhu Kila, mashawarcin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, gwamnan Jigawa kan watsa labarai, ya ce mai gidansa ya tarbi wadanda suka sauya shekar a wani taro da aka yi a gidan gwamnati a Dutse.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamnan Ya Takaita Atiku, Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Koma Bayan Tinubu

Jigawa LP to APC
Yan Takarar Majalisa 8 Na Jam'iyyar Labour Sun Koma APC A Shaharariyar Jihar Arewa. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kila ya ce wadanda suka sauya shekan sun fito ne daga Auyo, Kirikasamma, Bulangu, Malam Madori, Kafin Hausa, Birniwa, Guri da Kaugama.

Mashawarcin gwamnan ya kuma ambato Gwamna Badaru na cewa ba za a bar su a baya ba wurin gudanar da harkokin jam'iyyar APC a jihar.

Martanin wadanda suka sauya shekan

A bangarensa, Mohammed Makinta, dan takarar jam'iyyar LP na yankin Guri, ya ce shi da sauran yan takarar bakwai sun gano cewa APC ce "jam'iyya mafi nagarta."

Makinta ya ce:

"Mun yi alkawarin aiki domin ganin nasarar yan takarar jam'iyyar APC a babban zaben da ke tafe."

Aminu Sani Gumel, ciyaman din jam'iyyar APC a Jigawa, ya ce za a basu dukkan dama da hakki da tsaffin mambobin jam'iyyar APC ke mora.

Gumel ya ce:

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Takara 8 a Zaben 2023 Sun Jingine Tikitinsu, Sun Koma APC a Arewacin Najeriya

"A matsayin mu na yan jam'iyyar APC a yanzu, za ku amfana da duk wasu damarmarki da alfarma da wadanda kuka tarar a jam'iyyar ke da shi."

Dan majalisar dokokin jihar Gombe ya fita daga PDP ya koma jam'iyyar NNPP

A wani rahoton daban, Sani Dugge, dan majalisar dokoki a jihar Gombe, ya fita daga jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar NNPP.

Dugge, wanda ya wakilci mazabar Dukku West a majalisar dokokin jihar Gombe ya sanar da sauya shekarsa ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata na ranar 25 ga watan Disamban 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164