Tsohon Dan Majalisa a Gombe Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa NNPP

Tsohon Dan Majalisa a Gombe Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa NNPP

  • Tsohon dan majalisar dokokin jihar Gombe, Sani Dugge, ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa NNPP mai kayan marmari
  • Dugge, ya rubuta wasikar ficewa daga jam'iyar PDP zuwa ga shugaban jam'iya na yankinsa ɗauke da kwanan watan 25 ga watan Disamba, 2022
  • NNPP ta kara karfi sosai a 'yan makonnin nan a jihar Gombe, inda take da adadin mambobin majalisa kwatankwacin na PDP

Gombe - Tsohon mamban majalisar dokokin jihar Gombe, Sani Dugge, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa New Nigerian Peoples Party (NNPP).

Mista Dugge, wanda ya wakilci mazaɓar Dukku ta kudu a majalisar dokokin jihar ya sanar da matakim sauya shekarsa ne a wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 25 ga watan Disamba, 2022.

Tutar jam'iyar NNPP.
Tsohon Dan Majalisa a Gombe Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa NNPP Hoto: thecable
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto a wasikar, wacce ya aike wa shugaban PDP na Waziri ta kudu, tsohon ɗan majalisar ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Halaka Jigon Jam'iyyar PDP A Gidan Mahaifinsa

"Ina mai farin cikin sanar maka na yi murabus daga kasancewa na mamban PDP (Kati mai lamba 3528) daga yau ranar 25 ga watan Disamba, 2022."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa jigon siyasan ya zaɓi komawa NNPP?

Da yake tabbatar da matakin sauya sheƙarsa ga wakilin jaridar, Dugge ya bayyana dalilin komawa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari da wani abu na kai da kai.

A 'yan makonnin da suka shige, 'yan majalisar dokokin jihar Gombe guda uku suka sauya sheka zuwa jam'iyya NNPP.

Legit.ng Hausa ta gano cewa wannan ci gaban ya maida NNPP ta zama tana da adadin mambobi a majalisa dokokin Gombe daidai da yawan na jam'iyyar PDP.

Dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, yana ɗaya daga cikin manyan 'yan takarar da ake ganin zasu tabuka abin a zo a gani a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu

APC Ba Zata Samu Kaso 25 Na Kuri'un Jihata Ba Zan Iya Shiga Caca, Gwamnan Edo

A wani labarin kuma Gwamna Obaseki yace jam'iyyar APC ba zata ci kaso 25 cikin 100 na kuri'un Edo ba a 2023

Gwamna Godwin Obaseki yace babu kaffara a kansa idan ya rantse cewa APC ba zata samu kashi 25 cikin 100 na kuri'un jihar Edo ba a 2023.

Gwamnan, wanda yace Atiku zai samu nasara da gagarumin rinjaye, yace a shirye yake ya zuba dukiyarsa a caca kan cewa APC ba zata kai labari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel