An Tsaurara Tsaro Gabanin Zuwan Shugaba Buhari Adamawa Dan Halartar Yakin Neman Zabe

An Tsaurara Tsaro Gabanin Zuwan Shugaba Buhari Adamawa Dan Halartar Yakin Neman Zabe

  • Kamar yadda sanarwa ta gabata akwai wasu jihohi guda goma da shugaba Buhari zai ziyarcesu dan kaddamra da yakin neman zabe
  • Cikin jihohin akwai jihar Adamawa wacce take garin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar
  • Sen. Aisha Binani ce ke takarar gwamnan jihar a jam'iyyar APC mafi girman adawa a jihar ta Adamawa

Adamawa - Rundunar tsaron jihar Adamawa tace ta girke jami'an tsaro dan tabbatar da ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari zakai jihar.

Sannan rundunar ta bukaci da dai-daiku da masu fada aji da su bi umarnin ko sharadun da hukumar ta gindaya musu yayin ziyarar. Rahotan jaridar Daily Trust

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa SP Sulaiman Nguroje ne ya bayyana hakan a yammmacin yau asabar a babban birnin jihar Yola.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu Yana Taba Kirifto Ne: Yasha Alwashin Taimakon Yan Kirifto In Ya Kai Ga Gaci

Mai magana da yawun yan sandan ya kara da cewa aiyukan yan sandan zai karu wajen tabbatar da sun sa ido da kuma tafikar da komai cikin lumana

"Muna sa ran wannan jami'an tsaron zasu sa ido wajen tabbatar da komai ya saitu kuma yana kimtse kamar yadda aka tanada"

Sulaiman yace kwamishinan yan sandan jihar yana aiki kafada da kafada da al'ummar jihar dan ganin an samu zaman lafiya mai ddorewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan ya kara dacewa

"Rundunar yan sanda na kokarin ganin mun hada hannu da gwuiwa da al'umma wajen ganin mun samu abin da muke bukata"

Peoplesgazzate ta rawaito cewa kwamishinan yan sandan jihar da kansa ya fito yake kula da yadda aiyukan suke tafiya.

Binani
An Tsaurara Tsaro Gabanin Zuwan Shugaba Buhari Adamawa Dan Halartar Yakin Neman Zabe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sulaiman yace kwamishinann yan sandan ya umarci da a rage yawan zirga-zirgan ababen hawa, musamman ma a kusa da inda za'a gabatar da taron.

Kara karanta wannan

Yan Daba 61 hulumar yan sandan Jihar Kano Tayi Hole Kan Yunkurinsu Na Tada Tarzoma

Ya ce duk masu bi ta hanyar ko titin da zasi kaisu Filin tashi da saukar jirgin jihar da su bi ta unguwar Commissioner zuwa shataletalen Mubi.

Mai Buhari Zai je yi Adamawa?

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Shugaba Buhari zai isa birnin ne dan kaddamar da yakin neman zaben yar takarar gwamnan jihar wato Sanata Aisha Binani.

Tunda kafin wannan lokacin an ta samu sabani kan takarar ta ta, inda tsohon shugaban EFCC na Nigeria mallam Nuhu Ribadu ya kalubalanci takarar ta a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel