Tinubu Yasha Alwashin Taimakawa Yan Kiripto Idan Yakai Ga Gaci A Zabe

Tinubu Yasha Alwashin Taimakawa Yan Kiripto Idan Yakai Ga Gaci A Zabe

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC yasha alwashin taimakawa matsa masu harkar Kirifto
  • Bola ya bayyana cewa matasa na cikin na gaba-gaba da yake so ace ya taimaka muddin ya samu nasara a zaben 2023
  • Duk wata hanya ta taimakon matasa wadda kuma muka ga matasa na bin dan dogaro da kai tamuce kuma zamu taimaka musu

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu yace zai karfafi harkar hada-hadar kudi ta internet da kuma harkokin kirifto idan ya ci zabe

Harkar hada-hadar kudi dai ta intanet wata sabuwar hanya ce ta wallafa tare da ganin bayannan kudi da suke shige da fice. Rahotan jaridar The Cable

A shekarar 2021 babban bankin kasa CBN, ya umarci dukkan bankunan kasuwancin Nigeria da suk dakatar da duk wata mu'amala da zatai kama ko yanayi da hada-hadar kudi na kirifto.

Kara karanta wannan

Indai So Ake A Magance Matsalar Tsaro Da Satar Dukiyar Kasa To Atiku Ne zai Iya Magance Su, Tambuwal

Gwamnann Babbankin kasa yace anyi haka ne dan taimakawa yanyayin yan kasa wajen tabbatr da tsaron asusunsu.

Me Tinubu Yace Kan Batun Kirifto

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yayin da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC yake ganawa da matasa yayayi batu kan hada-hadar kudi ta kirifto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A juma'ar nan data gabata Tinubu ya bayyanawa matasa a Abuja cewa gwamnatinsa zata maida hankali kan yadda za'ai tsaruka da tsari mai kyau wajen inganta harkokin Intanet a kasar nan.

"Na muku alkawari za'a samu sabin tsarin tattalin arziki na zamani da kuma samar da damarmarki wanda za'aci moriyar intanet"
"Kuma zamu tabbatar da mun samar da hanyar da yan Nigeria zasu mori harkokin hada-hadar kudi ta kirifto dan samun riba da inganci mai yawa"

Jaridar The Cable ta rawaito cewa dan takarar bai tsaya a bayannin tattalin arziki kadai ba sai ya tabo batun aiyukan raya kasa inda yace:

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

Tinubu
Tinubu Yasha Alwashin Taimakawa Yan Kiripto Idan Yakai Ga Gaci A Zabe Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Nayi alkawari zan tabbatar mun inganta abubuwan more rayuwa, wanda suka hada da hanyoyin inganta harkar nishadantarwa, da bunkasa harkokokin samar da bayanai na nishadi ko fadakar da al'umma"

Bangaren Ilimi Nawa Ne Kuma Bazan Barshi A Baya Ba

A ganawar Tinubu bai gushe ba sai da ya tabo batun ilimi, inda yace zamu tabbatar da samar da shi mai inganci, mai nagarta, wanda za'asan lallae bangaren ilimi yana motsi a Nigeria.

"Nayi alkawari zan samar muku da ilimi dai-dai da karni na 21"

A karkashin muki na zakuyi mamakin yadda zan maida tattalin arzikin kasar nan da kuma yadda zan habaka shi, wanda haka zai kawo aiyukan yi da magance zamna banza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel