An Kama Yan Daba Da Suke Kokarin Tada Tarzoma A Yayinda Da Tinubu Ya Ziyarci Jihar

An Kama Yan Daba Da Suke Kokarin Tada Tarzoma A Yayinda Da Tinubu Ya Ziyarci Jihar

  • A ranar Talatan nan ne dai dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Tinu ya ziyarci jihar Kano yakin neman zabensa.
  • Kwanaki 49 ya rage a kada kuri'ar zaben shugaban pkasan Nigeria, wanda za'ai a ranar 25 ga watan biyu na wannan shekarar
  • Yan siysa da masu fada aji na amfani da yan daba domin biyawa kansu bukata, kamar yadda suke fada, ka tanadi mahaukacin karenka dan maganin mahaukacin karen wani.

Kano - Hukumar rundunar yan sandan jihar Kano ta yi holen wasu yan daba da suke kokarin tada zaune tsaye a yayin da ake tsaka da kamfen din dan takarar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinan yan sanda jihar Kano Muhammad Dauda yace kamensu na zuwa ne da kokarin yakar duk wani tada zaune tsaye da kuma ringingimun da ake shirin yi yayain lokacin zabe.

Kara karanta wannan

An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

Mai magana da yawun da yawun yansan jihar Kano kano yace an kama wanda ake zargin ne ranar 4 ga wannan watan da muke ciki. Rahotn The Cable

An dai kama wanda ake zargi din ranar da jam'iyyar APC take yakin neman zabe a jihar. zaku iya kallon bidiyon holen a kasa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar da Kiyawan ya fitar tace:

"An kama wanda ake zargin ranar 4 ga watan Janairun a yayin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar a kusa da filin wasan Sani Abacha dake kano"
"ya ce an samu wukake da adduna da barandami da almakashi a wiwi da sauran miyagun abubuwa a wajen yan daban"

Rundunar yan sandan jihar Kano tace zata tura yan daban gaban kuliya domin girbar abinda suka shuka.

Kara karanta wannan

Indai So Ake A Magance Matsalar Tsaro Da Satar Dukiyar Kasa To Atiku Ne zai Iya Magance Su, Tambuwal

A kokarin da hukumar yan sandan jihar Kano na ganin an tsaftace yadda bata gari da suke kokarin tashin hankali a jihar a lokacin zaben ko kuma kafin zabe.

Yan Siyasa Sunyi Alkawarin Taimakawa Wajen Wanzar Da Zaman Lafiya A Jihar Kano

Jaridar Daily Post tace Kamishinan yan sandan jihar Kano Muhammad Dauda yace:

"Yan siyasa da masu fada aji sun sa hannu a wata yarjejeniya da mukai da su a gaban kungiyoyi da hukumomin gwamnati kan tabbatar da zaman lafiya a yayin zabe"

Dauda ya kara godewa jama'ar jihar Kano Kan irin goyan bayan da suke bawa hukumar yan sanda da kuma irin fatan nasara da suke musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel