Babban Cikas Ga APC, Tinubu Yayin Da Shugaban 'Yarbawa' Ya Yi Maganan Karshe Kan Dan Takarar Shugaban Kasa

Babban Cikas Ga APC, Tinubu Yayin Da Shugaban 'Yarbawa' Ya Yi Maganan Karshe Kan Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Shugaban Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan goyon bayan da ya ke yi wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour
  • Shugaban na kungiyar Yarbawa, Pa Adebanjo ya ce ko da shugabannin kudu maso gabas sun ki goyon bayan Peter Obi, shi ba zai canja ra'ayinsa ba
  • A bangare guda, Obi na cigaba da samun goyon baya daga masu ruwa da tsaki a siyasar kasar wanda hakan na iya taimaka masa a zaben da ke tafe

Shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Ayo Adebanjo, ya ce ya goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi, don adalci da daidaito ne da hadin kai.

Adebanjo ya ce ko da dukkan mutanen yankin Ibo sun ki goyon bayan takarar Obi, shi da Afenifere za su cigaba da goyon bayansa saboda sunyi hakan ne don gaskiya, adalci, tarihi da daidaito.

Kara karanta wannan

Bayan Kwankwaso, Wani Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Yi Zazafan Martani Kan Goyon Bayan Peter Obi Da Obasanjo Ya Yi

Obi, Pa Adebanjo da Tinubu
Babban Cikas Ga APC, Tinubu Yayin Da Shugaban 'Yarbawa' Ya Yi Maganan Karshe Kan Dan Takarar Shugaban Kasa. Hoto: Pa Ayo Adebanjo, Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da yasa bana goyon bayan Tinubu, Pa Adebanjo ya magantu

A cewar jaridar The Guardian, shugaban na Afenifere, wanda ya musanta cewa ya ki jinin Tinubu, ya bayyana dalilinsa na kin goyon bayan takararsa, ya ce:

"Bana goyon bayan Tinubu saboda ba lokacin da kudi maso yamma bane."

Pa Adebanjo ya jinjinawa wa Obasanjo bisa goyon bayan Peter Obi

A yayin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya dauki matakin da ya dace a cewarsa.

"Mun dade muna fafutikan kare hakkin yarbawa tun kafin a haife wasu cikinsu. Yarbawa ba su cuta. Ba za ka kare hakkin yarbawa ta hanyar cutar wasu ba.
"Hakan ya yi kama da Atiku Abubakar, wanda ke kokarin zama shugaban kasa a lokacin da wani dan arewa ke shirin barin ofis. Shin kudu maso gabas ba cikin Najeriya ta ke ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Maidawa Obasanjo Martani a Kan ‘Dan Takaran da Yake Goyon Baya

Arewa ba ta da uzurin rashin goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, In Ji Ganduje

A bangare guda, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce mutanen arewa ba su da wani uzurin rashin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

Ganduje ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin cewa Shugaba Buhari ya dare kan mulki, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel