Kwankwaso Ya Bayyana Wata Gata Da Zai Yi Wa Daliban Najeriya Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa

Kwankwaso Ya Bayyana Wata Gata Da Zai Yi Wa Daliban Najeriya Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa

  • Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya ce daliban Najeriya za su dena biya kudin JAMB, WAEC da NECO idan an zabe shi
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma ce idan ya zama shugaban kasa jarrabawar JAMB za ta rika amfani na shekaru hudu a maimakon daya
  • Game da batun maja ko hadin kai da jam'iyyar Labour, Kwankwaso ya ce ya fi Peter Obi cancanta shi yasa bai yarda ya janye masa ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin biyan kudin WAEC, NECO da JAMB na dalibai idan an zabe shi shugaban kasa a zaben 2023.

A hirar da BBC Hausa ta yi da shi, ya ce idan aka zabe shi, sakamakon JAMB zai rika amfani tsawon shekaru hudu a maimakon daya.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

Kwankwaso
Kwankwaso: Dalibai Ba Za Su Biya Kudin WAEC, NECO Da JAMB Ba Idan Na Ci Zabe. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Mun saurari korafin mutane, duk inda muka tafi, muna yi wa mutane bayanin tsare-tsaren mu ga mutane musamman bangaren ilimi. Za mu gina makarantun firamari 500,000 cikin shekaru hudu.
"Za mu tabbatar yara miliyan 20 da ke yawa sun shiga makaranta, muna da shirin biyan WAEC, NECO ciki har da JAMB ga dalibai kuma JAMB zai rika amfani na shekara hudu a maimakon dalibai su rika sake rubutawa duk shekara idan ba su samu shiga makaranta ba."

Kwankwaso ya magantu kan hadin gwiwa a jam'iyyar Labour

A game da yiwuwar hadin kai da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Kwankwaso ya ce ya ki janye wa Peter Obi saboda ya fi shi kwarewa.

Ya ce:

"Shi (Peter Obi) gwamna kawai ya yi amma na yi ayyuka da dama; na yi aikin gwamnati na shekaru 17, bai yi ba, na yi mataimakin kakakin majalisar dokoki, bai yi ba. Ina cikin wadanda suka yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima, bai ya ciki.

Kara karanta wannan

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

"Baya ga wadannan, Na yi sanata, bai yi ba. Ko karatun mu ba daya bane idan ka duba, za ka gane cewa ba daya bane."

Arewa ba ta da uzurin rashin zaben Bola Tinubu - Ganduje

A wani rahoton, Dr Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya ce mutanen arewa ba su da wani uzurin rashin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a 2023.

Ganduje ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dare kan mulki, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164