Tashin Hankali Ga APC Yayin da Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Bi Sahun Su Atiku a Jihar Sokoto
- Jam’iyyar APC a jihar Sokoto ta yi babban rashi yayin da ta rasa wani jigo kuma babban danta, Faruk Malami Yabo
- Yabo ya taba tsayawa takarar gwamna a APC a jihar, inda ya rasa tikiti bayan zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar
- Gwamna Aminu Tambuwa da wasu jiga-jigan PDP ne suka karbi Yabo, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Jordan
Jihar Sokoto ¬Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Faruk Malami Yabo ya bayyana ficewa daga jam’iyyar tare da kama hanyar PDP ta su gwamna mai ci a jihar, Aminu Tambuwal.
Yabo, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Jordan ya bayyana shiga PDP ne a lokacin da tawagar kamfen din PDP ta dura karamar hukumar Yabo a jiya Laraba 4 ga watan Janairu.
Ya bayyana shigarsa PDP a matsayin dawowa gida, inda ya ce jinin PDP ne ke yawo a jikinsa, wacce ke mulkin jihar a Arewa maso Yammacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Sauya shekar daidai take da mutum ya dawo gida, Ina goodiya ga kowa da ke cikin wannan tafiya kuma na yi alkawarin taimawa jam’iyyar don ta yi nasara a zabe mai zuwa a jihar.”
Gwamna Tambuwal ta tarbi Yabo
Legit.ng ta tattaro cewa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne ya karbi Yabo zuwa PDP, kuma ya yaba masa da gano gaskiya.
A cewar gwamnan, shigowa Yabo PDP ya sanya ranar ta jiya a matsayin rana mai cike da tarihi ga siyasa da dimokradiyya a jihar Sokoto.
Jaridar Vanguard ta ruwaito Tambuwal na cewa:
“Dan uwa, bayyanawarka a hukunce ka dawo PDP, jam’iyyarka na ta jira kuma babban ci gaba ne a aikin da ke gabanmu.
“Wannan na ci gaba da nuna haske ga PDP cewa za ta yi nasara a jihar Sokoto da ma Najeriya baki daya.”
Obasanjo ya fi dukkan 'yan APC alheri, inji jigon siyasa
A wani labarin kuma, kunji yadda wani jigon siyasa a jihar su Tinubu ya yiwa Buhari da dukkan 'yan APC kudin goro, yace tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya fi su alheri.
Ya bayyana hakan ne a martaninsa ga yadda 'yan APC suka taso Obasanjo a gaba kan goyon bayan Peter Obi a zaben bana.
Kwanaki kadan suka rage a yi zabe a Najeriya, manyan kasa na ci gaba da bayyana wadanda suke goyon baya gabanin zaben.
Asali: Legit.ng