Babu Gwamnan APC Da Ya Hada Kai da Jam'iyar PDP, Atiku Bagudu

Babu Gwamnan APC Da Ya Hada Kai da Jam'iyar PDP, Atiku Bagudu

  • Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi yace baki daya gwamnonin APC na tare da burin Bola Tinubu na zama shugaban kasa
  • Bagudu, a wurin gangamin taron kamfen APC na Kano, ya musanta rahoton dake yawo cewa wasu gwamnoni na yi wa Tinubu zagon kasa
  • Dubun dubatar mutane ne suka halarci Ralin yakin neman zaben Tinubu a Kano ranar Laraba 4 ga watan Janairu, 2023

Kano - Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya musanta raɗe-radin cewa wasu gwamnonin jam'iyyar APC na aiki da tsagin adawa domin yakar burin Bola Tinubu na zama shugaban kasa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan ya yi tsokaci kan jita-jitar a wurin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a Kano ranar Laraba 4 ga watan Janairu, 2023.

Taron APC a Kano.
Babu Gwamnan APC Da Ya Hada Kai da Jam'iyar PDP, Atiku Bagudu Hoto: Dr. Abdullahi Ganduje/facebook
Asali: UGC

Gwamna Bagudu, shugaban kungiyar gwamnonin ci gaba na jam'iyyar APC kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka yi magana a gangamin, ya ce:

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce Ba Za a Gani a Kasa Ba, Tinubu Kan Alkawaran Zaben da Atiku da PDP Suka Daukarwa Yan Najeriya

"Dukkan gwamnonin mu suna tare da takarar Tinubu. Ikirarin da wasu mutane ke yaɗawa cewa wasu gwamnonin APC suna tattaunawa da jam'iyyar adawa karya ce."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nagode sosai - Tinubu

Da yake nasa jawabin, mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fada wa dandazon mutanen da suka tarbe shi cewa ya zo Kano ne ya yaba da goyon bayan da yake samu.

A wurin ralin arewa maso yamma da ya gudana a Kano, tsohon gwamnan jihar Legas ya jaddada yakininsa cewa shi ne zai zama magajin Buhari a zabe mai zuwa.

Tinubu, wanda ya yi takaitaccen jawabi a wurin, ya gode wa dubun dubatar Kanawan da suka nuna masa ana tare inda ya ce, "Nagode."

Ya kuma yi alƙawarin dawo da dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali idan aka zabe shi shugaban kasa a watan Fabrairu mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

"Na zo Kano abinda nake so kawai na dan taka rawa, zan samar maku da zaman lafiya da jituwa da juna zan yi wa Najeriya aiki tukuru. Nagode sosai," inji shi.

A wani labarin kuma Mai Magana da Yawun PCC ya ce Obi ne babban makamin da APC zata yi amfani da shi Tinubu ya zama shugaban kasa

Karamin ministan ƙwadugo kuma kakakin kamfen Tinubu/Shettima, yace duk wani mai hankali da nazari ya san an riga an gama zaben 2023.

Festus Keyamo yace Obi ya zama babban makamin da APC zata amfana da shi Tinubu ya lashe zaben domin ya raba kan magoya bayan Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel