Kwankwaso Ya Maidawa Obasanjo Martani a Kan ‘Dan Takaran da Yake Goyon Baya
- Rabiu Kwankwaso ya maidawa Olusegun Obasanjo da Edwin Clark raddi a kan goyon bayan Peter Obi
- ‘Dan takaran na jam’iyyar NNPP yana ganin ana nuna kabilanci da addini wajen goyon bayan ‘yan takara
- Kwankwaso ya ce jama’a ba za su biyewa Obasanjo ba wanda ya kamata ya daina nuna bambanci a zabe
Edo - ‘Dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi, Rabiu Musa Kwankwaso, ya maida martani ga Olusegun Obasanjo.
Channels TV ta ce maganar Rabiu Musa Kwankwaso ta biyo bayan wata wasika da Olusegun Obasanjo ya rubuta, inda ya nuna yana tare da Peter Obi.
Rabiu Kwankwaso wanda yake takara da Peter Obi, da Bola Tinubu da Atiku wajen neman shugabancin Najeriya a 2023 yana ganin hakan bai dace ba.
‘Dan takaran yana ganin bai kamata dattijo kamar tsohon shugaban kasar ko waninsa ya fito baro-baro, ya nuna ‘dan takaran da yake goyon baya ba.
Kwankwaso ya ziyarci Benin
Gidan talabijin ya rahoto Kwankwaso da ya je birnin Benin a jihar Edo yana cewa tsaida ‘dan takara zai iya jawo abin kunya ga wanda jagora ne shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina so in ba shugabanninmu shawara: su daina wulakanta kan su. Mu na matukar ganin girmansu. Idan ka ce ba ka so na, babu matsala."
- Rabiu Kwankwaso
Abin ya zama kabilanci?
Peter Obi ya samu goyon bayan dattawa daga kudancin Najeriya irinsu Olusegun Obasanjo da jagora a kungiyar PANDEF ta Neja Delta, Edwin Clark.
Vanguard ta rahoto Kwankwaso a ranar Laraba yana zargin cewa manya su na nuna bambancin addini da kabilanci wajen tsaidawa jama’a ‘dan takara.
Tsohon Ministan na Obasanjo ya ce talakawa sun yi hankali, ba za su biye masa ba.
"Wasu mutanen da suke goyon bayan wane ko wane su na tafka babban kuskure. Wadannan shugabanni ne da nake girmama masu.
Akwai lokacin da zai zo a rayuwa da za ka zama dattijon kwarai, ba ‘dan siyasa ba.
Ina mai tabbatar maku duk ‘dan takara ko jam’iyyar da ta zo da batun kabilanci ko addini, to ta fadi zabe tun kafin a kai ga kada kuri’u."
- Rabiu Kwankwaso
Wanene 'Yan G5 za su goyi baya?
A karshe dai kun ji labari watakila Gwamnonin G5 ba za su hada-kai, su marawa mutum daya baya domin ya zama Shugaban kasar Najeriya ba.
Gwamnonin za su yi la’akari da Jihohinsu, sai kowa ya wanke allonsa ta yadda zai samu goyon bayan mutanen da yake jagoranta cikin ruwan sanyi.
Asali: Legit.ng