2023: Alkawarin Karya PDP da Atiku Suke Daukarwa Yan Najeriya, Tinubu

2023: Alkawarin Karya PDP da Atiku Suke Daukarwa Yan Najeriya, Tinubu

  • Gabannin babban zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu ya ja hankalin yan Najeriya kan alkawaran zaben da Atiku Abubakar da PDP suka daukar masu
  • Dan takarar shugaban kasa na APC ya ce duk karya ce tanadin da babbar jam'iyyar adawa da dan takararta suka ce sun yiwa yan Najeriya
  • A cewar Tinubu, babu abun da PDP ta tsinanawa kasar tsawon shekaru 16 da ta yi a kan karagar mulki

Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Tinubu ya bayyana cewa Atiku da PDP na daukarwa al'ummar kasar alkawaran karya bayan sun gaza na tsawon shekaru 16, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku Zai Sauya Rayuwar Yan Najeriya Idan Ya Ci Zabe, Gwwana Tambuwal Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

Bola Tinubu
2023: Alkawarin Karya PDP da Atiku Suke Daukarwa Yan Najeriya, Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Sun kashe biliyoyi kan lantarki amma sun samar da duhu, Tinubu ya yi shagube ga PDP

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya fadi hakan ne a wajen wani gagarumin gangami da aka yi a Kano a ranar Laraba, 4 ga watan Janairu, jaridar The Cable ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bangare na jawabin Tinubu na cewa:

"Za mu iya inganta Najeriya, mu tsareta sannan mu kara wadata ta.
"Za mu iya ilimantar da matasanmu, mu ciyar da mutanenmu sannan mu kawo karshen fargaba. Za mu iya duk wadannan abubuwan. Za mu iya ci gaba.
"Amma saura ba za su iya ba. Suna son janka baya ta yadda su kadai ne za su iya ci gaba.
"Basa gabatar da komai sai alkawaran karya da amsoshi masu sauki da ba za a gani a kasa ba.

Kara karanta wannan

A Koreni Daga PDP Idan An Isa: Wike Ya Kalubalanci Uwar Jam'iyya

"Abun da za su iya nuna maka shine yadda za ka tsani dan uwanka dan Najeriya da kin aminta da makwabcinka.
"Amma ba za su iya nuna maka yadda za ka kare al'ummarka ba, ka ciyar da mutanenka, ka sama masu ayyukan yi da kula da wadanda ke tsananin bukatar taimako.
"Bara na fito karara na yi magana. Wannan kamfen ya kasance hadakarmu don inganta Najeriya. Shin muna tafiya gaba? ko muna makancewa a hanya?
“Dole ne mu ci gaba. Amma ba za mu taba mantawa da yadda suka bata mulkin kasarmu ba.
"Tsawon shekaru 16 suna wasa da rayuwarmu da makomar wannan kasa.
"Sun kashe dala biliyan 16 kan lantarki, amma sun samar da duhu a maimakon haka."

Dan takarar shugaban kasar ya lissafa wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin shugaban kaa Muhammadu Buhari ta samu a cikin shekaru takwas da ta yi tana mulki.

Ya kuma yi alkawarin daurawa a kansu da yin kari a kai.

A wani labari na daban, Bola Tinubu ya sha alwashin sauya fasalin Almajiranci tare da kafa wata hukuma ta musamman da za ta ja ragamarta idan har ya lashe zabe a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng