Atiku: Abin da Yake Shirin Faruwa da Gwamnonin G5 a Siyasa Inji Dino Melaye

Atiku: Abin da Yake Shirin Faruwa da Gwamnonin G5 a Siyasa Inji Dino Melaye

  • Sanata Dino Melaye yana ganin adawar ‘Yan G5 ba za ta hana Atiku Abubakar shiga Aso Rock ba
  • Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben PDP ya gargadi ‘Yan tafiyar G5 a PDP
  • ‘Dan siyasar ya ce ko da Gwamnonin ba su goyon bayan Atiku, ba za su iya hana mutane zaben shi ba

Abuja - Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar a PDP, Dino Melaye ya yi martani ga gwamnonin da ke cikin G7.

An samu baraka a jam’iyyar PDP inda gwamnoninta suka juyawa Alhaji Atiku Abubakar baya. Daily Trust ta ce Sanata Dino Melaye ya yi masu raddi.

Ganin ‘Yan G5 sun je Landan sun yi wani taro domin tsaida wanda za su marawa baya a zaben shugaban kasa, Dino Melaye ya ce ba za su kai labari ba.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya

Tsohon Sanatan kasar yana ganin wadannan Gwamnoni ba su da dalilin kin goyon bayan Atiku Abubakar ya zama shugaban Najeriya a zabe mai zuwa.

Babu dalilin yakar Atiku - Dino

"Su (Gwamnonin G5) ba su da wani dalilin cewa ba za su goyi bayan ‘dan takaran jam’iyyarsu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma na fitar da jawabi cewa idan suka ki goyon bayan ‘dan takaran shugaban kasarsu, kuma suka ce su na takara, to su shiryawa jana’izarsu.

Atiku
Yakin neman zaben PDP Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Kowane bangare na kasar nan, har da jihohin da suka fito da ‘yan takaransu da ‘yan jam’iyyarsu, har ‘yan APC za su goyi bayan takarar Atiku-Okowa.

Kusan (Gwamnoni) uku su na son zuwa majalisar dattawa a zaben 2023, daya daga cikinsu kuma yana so ya koma mulki a karkashin jam’iyyar PDP.

Ban san yadda za su bi, suyi watsi da ‘dan takaran shugabancin kasa na jam’iyyarsu, sannan su goyi bayan ‘dan takara daga wata jam’iyyar dabam ba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Babban Gwamnan PDP Yayi Ganawar Sirri Da Wike, Ortom a Fatakwal

'Yan G5 suyi hattara - PDP PCC

Wannan bakon abu ne a siyasar Duniya. Saboda haka ina bada shawarar khttps://admin.legit.ng/dashboarda da su kama wannan layi, idan kuwa suka yi haka, sun ci taliyarsu ta karshe.

Bayanin nan ya fito daga bakin tsohon Sanata na Kogi ne yayin da aka yi wata zantawa da shi a gidan talabijin Arise TV a karshen makon da ya wuce.

Wannan shi ne ra'ayin Don Pedro Obaseki wanda yake aiki da Atiku Abubakar. The Cable ta rahoto shi yana cewa gwamnonin za su dabawa kansu wuka.

Za a hana yara yin zabe a 2023

Rahoto ya zo ta bakin wani kwamishinan zabe cewa INEC za ta cafke yara 'yan kasa da shekara 18 a Duniya da iyayensu da suka nemi su kada kuri’a.

Festus Okoye ya shaidawa ‘Yan Najeriya kokarin da Hukumar INEC take yi wajen ganin an tsabtace zabe, an hana yaran da ba su girma ba jefa kuri’a

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Asali: Legit.ng

Online view pixel