2023: Hukumar INEC Ta Fadi Tanadin Ukubar da Tayi wa Kananan Yara Masu Yin Zabe
- Da zarar an samu wani yaron da bai kai shekara 18 ba a filin zabe, hukumar INEC za ta cafke shi
- Festus Okoye wanda Kwamishina ne a hukumar ya bayyana cewa za a kama har da iyayen yaran nan
- Okoye ya yi bayanin kokarin da INEC take yi wajen ganin an hana ‘yan kasa da shekara 18 yin zabe
Abuja - Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta watau INEC, ta yi alkawarin cafke duk wasu ‘yan kasa da shekara 18 da aka kama za su yi zabe.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar INEC, Festus Okoye ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin Arise.
Festus Okoye ya ce ana kokarin magance matsalar da ake samu ta ‘yan kananan yara su je su kada kuri’a, alhali sai ‘dan shekara 18 ne zai iya yin zabe.
Kwamishinan yake cewa a yunkurin ganin an tsabtace tsarin zabe, INEC ta taso duka jami’anta da aka samu ‘yan kananan yara sun yi rajista a wurinsu.
Za su bayyana a gaban wani kwamitin hukumar na musamman, kuma yanzu haka ana aikin.
"Mun kuma fito karara mun bayyana cewa za mu cafke duk wani wanda ake ganin bai kai shekarun zabe ba da muka gani a rumfunanmu a ranar zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan za a damke iyayensu da suka taimaka wajen wannan danyen aiki."
- Festus Okoye
Hukumar ta bakin kwamishinan, ta ce ana ta kokarin cire yara daga cikin rajistan zaben, kuma a karshe ‘Yan Najeriya za su ji dadin aikin da aka yi.
The Cable ta rahoto Okoye ya yi magana a kan kananan yaran da ake ganin hotonsu a rajistar INEC, ya ce wasu hotunan tun na zabukan 2011 ne.
A game da karbar katin zabe na PVC kuwa, Kwamishinan ya ce ba za a bari wani ya karbi kati da sunan wani ba, dole said ai mutum ya je ofishin da kansa.
Zuwa yanzu akwai mutane miliyan 93.5 da suka yi rajistar zabe a kasar nan. A ranar 16 ga watan Junairu ne INEC za ta fitar da rajista masu kada kuri’a.
Lafiya ta kalau fa… - Tinubu
Labari ya zo cewa ‘Dan takaran Shugaban kasa a APC mai mulki, ya ce an yi masa sharri ba zai iya tafiya ba, aka dawo ana cewa ba zai iya tsayuwa ba.
Bola Tinubu yake cewa da ya je aikin Umrah, ya yi zagayen dawafi sau bakwai, sannan ya hau dutsen Safa da na Marwa ba tare da taimakon kowa ba.
Asali: Legit.ng