Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya
- ‘Dan takaran Cif Olusegun Obasanjo a zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar nan shi ne Peter Obi
- Idan aka duba tarihi, za a fahimci goyon bayan da Obasanjo ya ba Atiku Abubakar a 2019 bai cece shi ba
- Tsohon shugaban Najeriyan bai iya kawowa Atiku da jam’iyyar PDP rumfarsa ba a Ogun, APC tayi nasara
Ogun - A ranar Lahadi, 1 ga watan Junairu 2022, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya fito baro-baro ya nuna yana goyon bayan Mista Peter Obi.
The Cable ta ce Cif Olusegun Obasanjo ya fadawa ‘Yan Najeriya ‘dan takararsa na zaben shugaban kasa ne a wata wasikarsa da ya fitar a sabuwar shekara.
Sai dai wannan mataki da tsohon shugaban kasar ya dauka bai ba mutane da-dama mamaki ba.
Jam’iyyun APC da PDP da ‘yan takaransu watau Bola Tinubu da Atiku Abubakar, har zuwa fadar shugaban kasa sun yi ta maidawa Cif Obasanjo martani.
Meya faru a zabukan 2019?
Jaridar The Cable ta bibiyi zaben shugaban kasa da aka yi a 2019, wanda Obasanjo a karon farko ya goyi bayan Atiku Abubakar, da kuma yadda ta kaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin inuwar PDP a zaben bana, shi ne mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Obasanjo.
A tsawon shekaru takwas da gwamnatin tayi daga 1999 zuwa 2007, Atiku ya rike wannan kujera, sai dai an samu rashin jituwa tsakanin shugabannin.
A zaben 2019, Cif Obasanjo ya ajiye gabarsu a gefe, ya marawa Wazirin Adamawa baya a kan Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC mai mulkin kasa.
APC ta doke PDP a akwatin Obasanjo
Idan za a tuna, wannan goyon bayan bai iya sa Atiku Abubakar ya doke Shugaba Buhari ba.
Abin mamaki a lokacin, Obasanjo bai iya kawowa Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP ko da akwatinsa ba, APC mai rike da kasar ce ta ba shi kunya a zaben.
Sakamakon zaben ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta sha mummunan kashi a rumfar zabe ta 22 da ke karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a Ogun.
A yayin da aka yi tunani tasirin Obasanjo zai yi aiki a zaben, sai ga tsohon mataimakinsa ya kare da kuri’u 18 rak, Muhammadu Buhari ya tashi da 87.
An murde zabukan 2003 - 2011
An ji labari an yi wata hira da ‘danuwan shugaban Najeriyan “Essential Muhammadu Buhari”, a nan ya yi bayanin abin da ya sa Muhammadu Buhari yin kuka.
Bayan shekaru 7 a kan mulki, Malam Mamman Daura ya fadi dalilin CPC na hadewa da ACN da APGA domin a doke jam’iyyar PDP daga kan karagar mulki
Asali: Legit.ng