Yan Daba Sun Faramki Ayarin Gwamna Aminu Tambuwal a Sokoto

Yan Daba Sun Faramki Ayarin Gwamna Aminu Tambuwal a Sokoto

  • Wasu tsageru sun farmaki Ayarin gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal a yankin karamar hukumar Wamakko
  • Lamarin dai ya auku ne yayin da tawagar gwamnan ke hanyar komawa daga gangamin kamfe a kananan hukumomi 2
  • Babu rahoton wani ya jikkata amma an ce duwatsun da aka jefa wa tawagar sun lalata wasu motoci

Sokoto - Yan daba sun kai wa Ayarin motocin gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, hari ranar Lahadin nan, 1 ga watan Janairu, 2023.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne lokacin da gwamna Tambuwal da wasu kusoshin gwamnatinsa ke kan hanyar dawowa daga wurin kamfe.

Aminu Waziri Tambuwal.
Yan Daba Sun Faramki Ayarin Gwamna Aminu Tambuwal a Sokoto Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

An ce 'yan daban sun farmaki Ayarin Tambuwal, darakta janar da kwamitin kamfen Atiku, yayin da zai koma gida daga wurin gangamin yakin PDP da ya gudana a kananan hukumomin Silame da Wamakko.

Kara karanta wannan

Sabuwar Shekara: Gwamna El-Rufai Ya Yi Wa Fursunoni 3911 Afuwa, Ya Taka Rawar Buga

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta ta ce maharan sun yi amafani da Duwatsu suka rika jifan motocin Ayarin mai girma gwamna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon jifa da duwatsun ne Gilashin kofar gaba na motar SUV ta mai ba Gwamna shawara ta musamman kan harkokin midiya ya farfashe.

Ya kara da cewa Duwatsun maharan sun yi raga-raga da gilashin gaba na motar babban Sakatataren gwamna, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Shin harin ya taba gwamna Tambuwal?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa manyan kusoshin PDP da ke cikin ayarin gwamnan ba su samu ko kwarzane ba sanadiyyar harin.

Baya ga gwamna Aminu Tambuwal, sauran wadan da ke cikin ayarin sun hada da mataimakin gwamna, Manir Muhamma Dan Iya, dan takarar gwamna a inuwar PDP, Saidu Umar, Abokin takararsa, Sagir Bafarawa da wssu jiga-jigai.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban Jam'iyyar PDP Yankan Rago a Jihar Arewa

Yan bindiga sun yi ajalin shugaban PDP a Sokoto

A wani labarin kuma Wasu miyagun 'yan bindiga sun je har gida sun halaka shugaban PDP ma Wata Guduma a Sakkwato

Wasu miyagu sun je har gida jim kadan bayan dawowa daga kamfen dan takarar gwamna, sun yi wa shugaban PDP na gundumar Asare yankar rago. Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun farmaki garin Asare, karamar hukumar Gwadabawa da babura akalla 16, suka tanka jigon PDP, suka halaka yayansa da ya kai masa ɗauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel