Babu Wata Ganawa da Nayi da Gwamnonin G-5 a Landan, Tinubu Ya Fasa Kwai
- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya fasa kwai game da wata jita-jita da ke yawa a Najeriya
- A cewar rahotanni a kasar nan, an yi wata ganawar sirri tsakanin Tinubu da wasu gwamnonin PDP masu adawa da Atiku
- A halin yanzu, Tinubu na can a kasar Saudiyya inda yake gudanar aikin Umrah, ya kuma ce kamfen ne abin da yasa a gabansa
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi watsi da batun ganawar sirri da gwamnonin G-5 na PDP masu adawa da Atiku a birnin Landan.
Ya kuma bayyana cewa, rahotannin da ake yadawa a kai suna dauke da mugun nufi da kuma manufa ta yada barna mai yawa, The Nation ta ruwaito.
Dan takarar na APC, wanda a yanzu haka yake gudanar Umrah a kasar Saudiyya ya ce, wasu baragurbi ne suka wallafa rahoton don tallata aniyarsu ta siyasa da kuma yiwa wadanda ke daukar nauyinsu aiki.
Dalilin da yasa Tinubu ya fasa kwai
A cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar ta hannun hadiminsa, Tunde Rahman a Abuja, ya ce babu abin da ya saka a gabansa yanzu kamar batun kamfen a fadin kasar nan, This Day ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar sanarwar:
“Yayin da yake Landan, Asiwaju Tinubu ya gano wasu rubuce-rubuce da ke yawo a gidajen jaridun Najeriya da ke zargin ya yi ganawar sirri da gwamnonin G-5 wadanda mambobin jam’iyyar PDP ne.
“Wadannan rahotanni, a takaice, ba ma an yi su da mummunan imani bane kadai, bal ma an yi su da mugun nufi ne.
“An buga su ne don habaka muradin siyasar marubutan da masu daukar nauyinsu.
“Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, mai girma Asiwaju Tinubu bai damu da wadannan rahotannin ba balle masu daukar nauyinsu da suke sanannu.”
Bayani Ya Fito Bayan Rahotanni da Ke Cewa Gwamnonin G5 Sun Gana da Tinubu a Landan
Bayanai sun fito daga wata majiya kan yadda ganawar Tinubu da gwamnonin PDP ta kankama, duk da cewa ana ta cece-kuce.
Wani rahoton Punch ya bayyana cewa, an yi ganawar Tinubu da gwamnonin PDP na G-5, an ce sun yi magana kan zaben 2023.
Gwamnonin sun ce ba za su yi goyon bayan wani dan takara ba a yanzu saboda wasu dalilai da ke kasa,
Asali: Legit.ng