PDP Zata Ladabtar Da Wike Lokacin Da Ya Dace -Gwamna Tambuwal

PDP Zata Ladabtar Da Wike Lokacin Da Ya Dace -Gwamna Tambuwal

  • A na tsaka da jita-jita kan wanda Wike zai marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa, gwamnan yasha gargaɗi daga takwaran sa na jihar Sokoto
  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace jam'iyyar a shirye take da ta ɗauki matakin ladabtarwa ga dukkanin ƴaƴanta marasa biyayya
  • Tambuwal ya kuma bayyana haƙiƙanin lokacin da jam'iyyar zata ɗauki mataki akan su Wike

A yayin da ake ta jita-jita kan ɗan takarar shugaban ƙasa wanda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, zai marawa baya a 2023, takwaran sa na jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yayi masa martani mai ƙaushi.

Tambuwal yace jam'iyyar tana da hurumin dokar ladabtar da waɗanda suka yi mata ba daidai ba.

Tambuwal
PDP Zata Ladabtar Da Wike Lokacin Da Ya Dace -Gwamna Tambuwal
Asali: Facebook

Aminu Waziri Tambuwal ya aike da saƙon gargaɗi zuwa ga gwamnan na jihar Ribas da sauran waɗanda suke son suyi jayayya da abinda jam'iyyar PDP ke muradi. Rahoton Channels TV ya tabbatar.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Yayi Kasuwa A Katsina, Ƙungiyoyi Sama da 70 Sun Gudanar Tattakin Nuna Goyon Baya

Hadimin Tambuwal na ɓangaren watsa labarai, Muhammad Bello, a wata sanarwa ranar Juma'a ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jam'iyyar PDP za tayi martani kan soki burutsun da gwamnonin ta biyar keyi wanda ake jita-jitar sun ƙulla alaƙar siyasa da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu."
"Tsawon sa'o'i kafin bayanin sa akwai rahotanni dake cewa gwamnonin G5 ƙarƙashin Wike, sun yi tarurruka da Tinubu a birnin Landan akan yiwuwar haɗewa da shi domin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa."
"Jam'iyyar PDP jam'iyya mai biyayya ga doka, sannan za tayi amfani da tsarin doka wajen hukunta dukkanin ƴaƴanta masu aikata laifi."

Tambuwal ya kuma ce yana tattaunawa ta siyasa da ƴan tawagar ta G5, waɗanda ya bayyana a matsayin "takwarori nagari."

Ya ci gaba da cewa:

"Ko kaɗan ba yaƙi bane. Na ɗauki hakan a layin mu na siyasa, duk abinda kake yi koda kayi ƙoƙarin boyewa, sai ya fito. Ba zaka iya wani shiri na siyasa da aiwatar da shi a ɓoye ba. Dole sai ka bayyana shi."

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Ya Karaya, Ya Faɗi Wanda Zai Lashe Zaben 2023 Idan G-5 Suka Koma Bayan Tinubu

"Saboda haka duk lokacin da takwarorina suka yanke abinda za suyi, ina tunanin a lokacin ne jam'iyyar za tayi martani kan matsayar da suka cimmawa. A cewar sa"

Wike Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa, Ya Bayyana Gaskiya Kan Halin Da G5 Ke Ciki

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya fito fili ya bayyana gaskiya game da jita-jitar da ake yaɗawa kan ƙungiyar su ta G5.

Jita-jita na ta yawo kan cewa ƴan ƙungiyar ta G5 sun cimma yarjejeniya da ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa domin mara masa baya ya kai ga nasara a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel