‘Dan Kwamitin Yakin Neman Zabe Ya Yi Magana a Kan Lamarin Lafiyar Bola Tinubu

‘Dan Kwamitin Yakin Neman Zabe Ya Yi Magana a Kan Lamarin Lafiyar Bola Tinubu

  • Kwamred Adegboye Adebayo yana ganin manufofin Bola Tinubu sun fi na kowane ‘dan takaran 2023
  • Adegboye Adebayo ya ce abin da ya kamata mutane su maida hankali a kai shi ne manufofin ‘yan takara
  • ‘Dan kwamitin neman zaben ya yi watsi da jita-jitar cewa Tinubu bai da isasshen lafiyan da za iyi mulki

Osun - Wani daga cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Adegboye Adebayo ya ce Bola Tinubu zai magance matsalolin Najeriya.

Vanguard ta rahoto Kwamred Adegboye Adebayo yana mai cewa manufofin da Bola Tinubu ya kawo, za su kawo gyara idan har aka zabe shi a APC a 2023.

Da yake magana da manema labarai a makon nan, Adebayo ya ce akwai bukatar mutanen Najeriya su duba manufofin da ‘dan takaran na su ya zo da su.

Kara karanta wannan

Yadda Bola Tinubu Ya Kawo Karshen Mummunan Rikicin Jam’iyyar APC Cikin Ruwan Sanyi

Adebayo wanda shi Sakataren yada labarai na kungiyar Asiwaju Project Beyond 2023 ya yi tir da yadda ake yawan surutu a kan maganar halin lafiyar Tinubu.

Tinubu ya yi an gani a baya - Adebayo

‘Dan siyasar yana ganin mutane sun saki reshe ne sun kama ganye domin ba batun koshin lafiyar ‘dan takaran ake yi ba, ayyukan da ya yi a baya za a duba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan aka kwatanta shi da sauran ‘yan takara, manufofin Bola Tinubu sun kawo mafita ga manyan matsalolin da suke adabar Najeriya a yau.

Matsalolin nan su ne samar da wutar lantarki da raba shi, matsalar rashin tsaro, harkar aikin ‘yan sanda da yi wa tsarin kasa garambawul.
Mu na kira ga dinbin masu kada kuri’a su duba yadda za a kula da cigaban kasa, tsaro, kiwon lafiya da ilmi.

Kara karanta wannan

Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Gamu da Kalubale a Takarar Shugabancin Najeriya

Tarihi ya nuna Bola Tinubu ya sha gaban kowa a wajen sauke alkawuran da ya dauka a wajen yin kamfe.

- Adegboye Adebayo

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima wajen kamfe Hoto; gazettengr.com
Asali: UGC

Aikin da ke gaban APC PCC

Sun ta rahoto ‘dan kwamitin yakin zaben yana cewa abin da ya rage masu shi ne a fahimtar da mutanen karkara wadannan manufofi na ‘dan takaran APC.

Adebayo ya ce Tinubu yana da kwarin lafiyar da zai rike ofishin shugaban kasa domin tun da ya fara kamfe, yake yawo duk wani lungu da sako a Najeriya.

"Saboda kurum an yi masa aiki a gwiwa bai nufin ba zai iya shugabantar Najeriya ba. Yana takara ne domin kwakwalwarsa garau ta ke, kuma yana da basira.
Yana cikin koshin lafiya, yana da basirar da zai jagoranci kasar nan, babu maganar rashin lafiyar da za ta tsaida shi.”

- Adegboye Adebayo

Bola Tinubu yayi abin da ya gagari kowa

John Owan Enoh ya je kotu har uku yana kara a kan takarar Gwamna da Jam’iyyar APC ta ba Sanata Bassey Otu, an ji labari cewa ‘dan takaran ya hakura.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP Suka Hadu da Tawagar Tinubu Ta Bayyana

Ganin Asiwaju Bola Tinubu da kan shi ya roke shi a gaban jama’a, Sanata Enoh ya fasa shari’a da jam’iyyarsa, yanzu zai yi wa APC aiki ne a zaben badi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng