Tayi Tsami: An Gano Wanda Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Yake Goyon Baya a 2023
- Jam’iyyar Labor Party ta tabbatar da cewa tana da goyon bayan Olusegun Obasanjo a zaben 2023
- Akin Osuntokun ya ce tsohon shugaban kasar yana cikin wadanda ke marawa Peter Obi baya a LP
- Darektan yakin neman zaben ya yi karin haske a kan alakarsa da Doyin Okupe da takararsa a ZLP
Abuja - Sabon Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben Peter Obi a jam’iyyar LP, Akin Osuntokun ya ce Olusegun Obasanjo yana tare da su.
Da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Akin Osuntokun ya nuna su na da goyon bayan tsohon shugaba Olusegun Obasanjo.
An tambayi Osuntokun ko tsohon shugaban na Najeriya ya ba Obi cikakken goyon bayan zama shugaban kasa a 2023, sai amsa da haka abin yake.
Channels ta tattauna da sabon Darektan yakin neman zaben ne jim kadan bayan ya shiga ofis.
Doyin Okupe tamkar Uba ne a wurinmu
Osuntokun ya bayyana alakarsa da Dr. Doyin Okupe wanda ya gada a matsayin ta uba da ‘ya ‘yansa, ya ce tsohon Darektan tamkar uba yake a gare su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Osuntokun ya nuna Dr. Okupe ya fi karfin a kira shi abokin aiki, sannan yake cewa ya cancanta ya rike kujerar Darektan yakin takarar shugaban kasa.
Wasu na ganin cewa sabon Darekta Janar din bai kamata ya dare wannan kujerar ba, amma ya musanya hakan, ya ce karin matsayi kurum aka yi masa.
"Ka da a manta ni ne tsohon shugaban yakin neman zabe a yankin Kudu maso yamma, saboda haka kamar karin matsayi ne.
Ba wai yanzu na shigo kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba, amma idan ka ce kujerar Obasanjo ce, to shikenan."
- Akin Osuntokun
Tsohon hadimin na Olusegun Obasanjo ya fadawa gidan talabijin cewa abin da ya kamata a duba shi ne kokarin da za iyi wa LP ba wanda ya kawo shi ba.
'Dan ZLP ya zama DG a LP?
Sahara Reporters ta rahoto Osuntokun yana cewa ya yi watsi da takarar Sanata da yake yi a karkashin Jam’iyyar ZLP tun da ya zama Darektan kamfen LP.
‘Dan siyasar ya ce ZLP ta fitar da jawabi a kan janye takararsa, kuma ba a sabawa wata dokar kasa da nadin ba. Jaridar Vanguard ta fitar da wannan rahoto.
Rikicin G5 da Atiku Abubakar
An ji labari cewa Gwamnonin da ke yakar Atiku Abubakar sun ki bari ayi sulhu da kowa, hakan ya sa suka zauna da Bola Tinubu da manyan Jam’iyyar APC.
A taron sirrin da Gwamnonin na PDP suka yi da wakilan ‘dan takaran shugaban kasa na APC a kasar waje, sun duba wanda za su marawa baya a zaben badi
Asali: Legit.ng