Jam’iyyar APC Ce Za Ta Tabbatar da Fara Aikin Hako Mai a Kolmani, Inji Gwamna Yahaya Na Gombe

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Tabbatar da Fara Aikin Hako Mai a Kolmani, Inji Gwamna Yahaya Na Gombe

  • Gwamnan jihar Gombe ya bayyana irin kokarin da ya yi wajen tabbatuwar aikin hakon mai a Kolmani
  • Gwamnan ya ce gwamnatin APC ce ta tabbatar da wannan aikin, kuma sake ba ta dama zai sa a iya yin aikin
  • Ya godewa Buhari, ya ce mutanen Gombe za su fara cin moriyar rijiyoyin Kolmani nan ba da jimawa ba

Pindiga, jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe ya bayyana kwarin gwiwar cewa, jam’iyyar APC za ta yi aikin tabbatar da hako man fetur a Arewacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Alhaji Muhammadu Inuwa ya bayyana cewa, APC za ta tabbatar da aikin hako gadan-dagan a rijiyoyin man Kolmani da aka samo, wadanda Buhari ya kaddamar a watan jiya.

Gwamna Inuwa ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wata ziyara a masarautar mai martaba sarkin Pindiga, Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad a shirye-shiryen kamfen dinsa na 2023.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

APC za ta tabbatar an hako mai a Arewa
Jam’iyyar APC Ce Za Ta Tabbatar da Fara Aikin Hako Mai a Kolmani, Inji Gwamna Yahaya Na Gombe | Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

A cewarsa, a karkashin gwamnatin APC nasa, zai tabbatar da faruwar kowane aiki da ya dauko gadan-dagan don inganta rayuwar talakan jihar Gombe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu tabbata aikin Kolmani bai sha ruwa ba

Hakazalika, ya ce gwamnatinsa na aiki da masu ruwa da tsaki da suka dace wajen tabbatar da aikin hakon mai a Kolmani bai zama labarin ‘yan baya kuma shafaffe a kundin tarihi ba.

Jaridar Leadership ta ruwaito gwamna Inuwa na cewa:

“Watanni biyu kacal da muka karbi mulki, muka fara kai komo daga kamfanin man fetur na Najeria (NNPC) zuwa fadar shugaban kasa don tabbatuwar aikin Kolmani, kuma Alhamdulillahi mun yi nasara samun aikin.
“Muna godiya ga shugaban kasa Muhammadu da ya tabbatar da faruwar wannan aikin.
“A bangarenmu, mun yi duk mai yiwuwa don tabbatar da aikin nan ya tsaya a Gombe, kuma dukkanku shaidu ne an kaddamar da aikin kuma muna fatan al’ummarmu za ta fara cin moriyarsa nan gaba kadan.”

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Dau Alkawarin Gina Masallaci da Coci a Wani Kauye

Yadda aka kaddamar da mahakar mai a Arewa

A tun farko kun ji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagorancin manyan kasar nan wajen kaddamar da rijiyoyin mai da aka tona a jihar Gombe.

Mahakar man Kolmani ce ta farko a Arewacin Najeriya, kuma ‘yan yankin sun jima dakon wannan babban rana na samar da mai a Arewa.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan babban taro akwai dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.