Kotu Ta Sa Ranar da APC, Tinubu Za Su San Makomarsu a Kan Takara a Zaben 2023

Kotu Ta Sa Ranar da APC, Tinubu Za Su San Makomarsu a Kan Takara a Zaben 2023

  • Kotu ta saurari karar da Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International ta kai
  • Kungiyar ta bukaci kotu ta umarci Hukumar INEC ta cire Asiwaju Bola Tinubu daga cikin masu takara a 2023
  • ‘Dan takaran na All Progressives Congress (APC) yana so a watsar da karar domin ya iya zama shugaban kasa

Abuja - Bola Tinubu mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki ya nemi ayi watsi da karar hana shi shiga takara.

Vanguard ta ce a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba 2022, Bola Tinubu ya roki kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta jefar da kararsa da aka shigar.

Lauyan da ya tsayawa ‘dan takaran na APC, Karma Fagbemi ya fadawa Mai shari’a Karma Fagbemi cewa wadanda suka kai karar ba su da hurumi.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu

Kungiyar Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International mai so a hana Tinubu takara ba jam’iyyar siyasa ko ‘dan takara ba ce.

Babu ruwan masu kara da APC

Fagbemi ya ce babu dalilin da kungiyar za ta tsoma baki a kan abin da ya shafi siyasar APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar The Guardian ta ce Lauyan da yake kare jam’iyyar APC a kotun tarayyar, Ibrahim Audu ya yi wa Alkali irin wannan bayani da kotu ta zauna.

Bola Tinubu
Bola Tinubu mai takara a zaben 2023 Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Inda APC ta saba doka - Lauya

Lauyan da ya shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1960/22, ya kafa hujja da sashe na 84(13) na dokar zabe, yana so INEC ta hana Tinubu takara.

Kungiyar ta na ganin APC ta saba sashe na 91(3) na dokar zaben kasa, wanda ya hana jam’iyya karbar gudumuwar da ta fi N50m ba tare da an yi bayani ba.

Kara karanta wannan

Magoya Bayan Jonathan Sun Tsaida ‘Dan Takara, Sun Shiga Yi wa Tinubu Kamfe a Kudu

Bola Tinubu mai harin kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben badi, ta bakin Lauyansa, Lateef Fagbemi SAN ya kalubalanci karar nan da aka shigar.

Rokon Bola Tinubu a kotu

An rahoto Fagbemi SAN yana cewa babu hujjar da ke gaskata zargin masu shigar da kara, kuma an dauki tsawon kwanaki 14 ba su iya gabatar da hujja ba.

Ganin lokaci ya wuce ba tare da Incorporated Trustees of Kingdom Human Rights Foundation International ta gamsar da kotu ba, an roki ayi waje da karar.

Bayan sauraron Lauya mai kara, Johnmary Jideobi da sauran masu bada kariya, Alkali Nyako ta tsaida 27 ga Junairu a matsayin ranar da za a yanke hukunci.

Abin da ya sa nake goyon bayan Tinubu

Labari ya zo cewa ‘Yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Tinubu APC sun taka har zuwa gidan Sanata Chimaroke Nnamani a jihar Enugu.

Sanatan na gabashin Enugu ya fayyace dalilin yi wa Atiku Abubakar adawa, yake goyon bayan takarar Tinubu alhali shi 'dan jam'iyyar adawa ta PDP ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng