Na Cika Alkawurran Da Na Daukarwa Mutanen Jigawa A Kamfe, Badaru

Na Cika Alkawurran Da Na Daukarwa Mutanen Jigawa A Kamfe, Badaru

  • Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, yace bai rage ko kwara daya ba ya cika alkawurran da ya dauka kafin hawa mulki
  • Badaru ya bayyana cewa bayan cika alkawari ya kara da muhimman ayyuka da tsare-tsaren walwala ga al'umma
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan ke gab da kare wa'adin mulkinsa na biyu a shekarar 2023

Jigawa - Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, yace ba ya nadamar zangon mulkinsa biyu tun daga 2015 domin har yanzu talakawa na kaunarsa kuma suka ganin grimansa.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa gwamna Badaru ya yi wannan jawabin ne yayin da yake zantawa da 'yan jarida a Ofishinsa da ke Dutse, babban birnin Jigawa.

Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru.
Na Cika Alkawurran Da Na Daukarwa Mutanen Jigawa A Kamfe, Badaru Hoto: leadership
Asali: Facebook

Gwamnan wanda ya hau kan mulki a shekarar 2015 karkashin inuwar APC, yace ya yi nasarar aiwatar da muhimmin aiki aƙalla guda ɗaya a kowane yanki dake Jigawa.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

Na cika baki ɗaya alkawurran da na ɗauka - Badaru

Badaru ya ƙara da cewa bai bar ko sili ɗaya ba ya cika dukkanin alkawurran da ya ɗauka lokacin yakin neman zabe har ma ya dora da karin muhimman ayyuka da tsare-tsare waɗanda suka sa walwala a fuskar talakawan Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa ya ce:

"Ina da yakinin kowa shaida ne cewa gwamnatin APC ta aiwatar da ayyuka masu nagarta wanda ya ɗaga darajar jiharmu har ta shiga cikin jihohin dake jan hankalin masu zuba jari, ga Tituna masu kyau a ko ina."
"Mune a matsayin farko a ɓangaren samar da ruwa mai tsafta a arewacin Najeriya Kuma mune na biyu a ƙasa baki ɗaya. Noman da muke ya karu da sama da kaso 100, ilimi ya haɓaka da kaso 60, haka tattalin arzikin mu ya nunka 2."

Kara karanta wannan

Babu Nakasasshe Sai Rage: Bidiyon Mai Nakasa Yana Kasuwanci A 'Yar Kekensa

"Mun cimma akalla a kowace gunduma ɗaya akwai wurin duba lafiya yayin da tsarin mu na samar da ilimin 'ya'ya mata da tallafin karatu ya kara mana yawan kwararru a ɓangaren lafiya da sauransu."

Mutanen Jigawa sun yaba da kokarin mu - Badaru

"Ina kara gode wa Allah, mutane suna yaba wa da shugabancin mu, hakan ya bani karfin guiwar yawon neman a sake zaɓen APC," inji Badaru.

Gwamnan ya jaddada kudirinsa na barin asusun Jigawa makare da arziki ga wanda zai gaje shi ba kamar yadda ya zo ya samu ba.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani mazaunin karamar hukumar Birnin Kudu, jihar Jigawa, Aminu Aminu Majeh, yace gwamna Badaru ya yi kokari a mulkinsa.

Malam Aminu, wanda ya kammala digirinsa na faro, ya ce ba zai iya cewa Badaru ya cika duka alkawurran da ya dauka ba amma tabbas ya cika mafi yawa.

A cewarsa, matsalar da gwamnan ya samu ta fi tattaruwa a bangaren ilimi, inda ya shaida wa wakilin mu cewa:

Kara karanta wannan

2023: Gaskiya Ta Fito, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rahoton Yana Yi Wa PDP Aiki

"Yayi kokari gaskia sosai, wajen da yasamu nakasu wajen diban ma'aikata ne, yawancin ma'aikatan Jigawa sun aje aiki Amma ba'a maye gurbin su ba, makarantun mu duk ba malamai."

Da wakilin mu ya tambaye shi ko yana ganin jam'uyyar APC zata iya samun nasara a zabe mai zuwa, Aminu ya amsa da cewa, "Eh ina da yakinin haka."

A wani labarin kuma Gwamna Inuwa Yahaya Ya Fallasa Asirin Yan Siyasan Da Basu Son Amfani da BVAS a 2023

Yayin kamfen APC a yankin Garko, gwamnan jihar Gombe dake neman ta zarce yace ko kaɗan ba ya jin tsoron amfani da BVAS a zabe mai zuwa.

Yace na'urar ta zo ne domin maganin yan siyasar dake dogara da magudin zabe, domin a cewarsa wannan ba Card Reader bace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262