"Ana Jin Jiki a Kasar Nan": Bidiyon Mai Nakasa Yana Kasuwanci A 'Yar Kekensa

"Ana Jin Jiki a Kasar Nan": Bidiyon Mai Nakasa Yana Kasuwanci A 'Yar Kekensa

  • Wani mutumi mai nakasa ya mayar da keken tafiyar wata kwarya-kwaryar shago a Mushin jihar Legas
  • Wani mai amfani da shafin Tikok ya dauki bidiyonsa domin nunawa mutane ko mutumin zai samu taimako
  • Mutane da dama sun jinjinawa nakassashen inda suka ce kasar nan fa kowa na ji a jikinsa dole a tashi tsaye

Legas -Wani matashi ma'aboci kafar sada zumuntar TikTok ya na'di bidiyon wani nakasasshe wanda ya mayar da keken tafiyar shagon sayar da kaya.

Wannan bidiyo da aka daura tun ranar 27 ga Disamba ya yadu matuka a kafafen ra'ayi da sada zumuntar yanar gizo.

Mutum cikin farin ciki da annashawa yana tura kekensa kuma yana sayarwa mutane abubuwan da yake dauke da su.

Mushin
"Ana Jin Jiki a Kasar Nan": Bidiyon Mai Nakasa Yana Kasuwanci A 'Yar Kekensa Hoto: TikTok/@untitledrichway
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Rudani: Dalibin Aji 3 a Jami’a ya Gane Babu Sunansa a Rijistar Jami’a Baki Daya

Vincent Chika wanda ya daura bidiyon a shafinsa na Tiktok ya bayyana cewa ya ga mutumin ne a unguwar Mushin ta jihar Legas.

Kwana daya kacal da daura bidiyon, ma'abota TikTok sun fara shawaran yadda za'a taimaka masa da tallafi.

Chika yace a kan bidiyon:

"Gaskiya ya bani tausayi. Ina masa addu'a Allah ya sa ya samu cigaba kuma sauki."

Kalli bidiyon:

Martanin mutane:

Zakariyya Gambo yace:

"ALLAH ya kawomana saukin rayuwar a nigeria da ma duniya ga ba dayan ta"

Mubarak Kabir yace:

"Wannan sanin ciwon Kaine ba Jin jiki bane
Hakan ya fiye mishi bara da maula✊
Kamar yadda wasu masu nakasa irinshi sukeyi wasu lokutan harda masu lafiyarma"

Lukman Abbas yace:

Bamaganan shan wahala a kan wannan,yanda yakamata murayu don naiman nakai ba rukoba ko bara ba.Allah ya masa jagora amin.

Yaseer M Arab:

Wannan ne jin jikin, Ya fito yana neman na kansa Wato kunfiso yayi bara ko

Kara karanta wannan

Ya Kashe Kudi Sosai a Kai: Dan Najeriya Ya Tuka Motar G-Wagon Da Ya Kera Da Kansa a Bidiyo

Bello Musa D-daji:

Ya birgeni domin yafimasa yawon bara ana wulakantashi, Allah SWT ya karama sana'ar Albarka

Dogara Musa:

A gaskiya akwai masala domin kuwa a yanzu haka masara tana 20k thousands

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags:
Online view pixel