Wike da Gwamnonin PDP Hudu Zasu Gana da Bola Tinubu Game da 2023
- Wasu bayanai sun nuna cewa Bola Tinubu zai gana da gwamnoni G5 da suka ware kansu a PDP domin karkare zance
- An ce gwamnonin karkashin jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun tafi Burtaniya
- Yanzu abinda ake dako a ji shi ne wane ɗan takara gwamna Wike zai ambaci sunansa a watan Janairu kamar yadda ya ɗau alkawari
Abuja - Domin karkare komai kan kujerar shugaban kasa a 2023, gwamnoni 5 na PDP da suka fusata zasu zauna da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wata majiya mai kusanci da tsohon gwamnan Legas ta ce matukar ba a samu sauyin bazata ba, taron zai gudana ne a ɗaya daga cikin kasashen turai.
Majiyar wacce ta ƙi bayyana ainihin ranar ganawar bangarorin biyu, ta kara da cewa an shirya ganawar ne domin kara jaddada yarjejeniya kan zaɓen shugaban ƙasan 2023 tare da gwamnonin 5.
Yace bayan wannan zama ne gwamnonin da ake kira tawagar gaskiya ko G-5 zasu bayyana ɗan takarar shugaban ƙasar da zasu wa aiki domin kowa ya sani.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamnonin G-5 sun haɗa da, Nyesom Wike (Ribas), Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benuwai), Okezie Ikpeazu (Abiya) da kuma Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).
Wasu rahotanni sun nuna cewa yanzu haka gwamnonin suna kasar Birtaniya gabanin taronsu da Bola Tinubu. Majiyar tace:
"Goyon bayan da Tinubu zai samu daga gwamnonin G-5 zai sauya wasan, irin haka jam'iyyar APC ta samu daga tawagar G6 a 2014. Zamu gana da tawagar a Turai wannan makon domin karkare yarjejeniya."
"Akwai masu kishin ƙasa na ajin farko waɗan da kishin Najeriya suka sa gaba fiye da komai kuma ya dace mu haɗa kai domin ƙasar mu ta yi kyau."
Tun bayan zaben fidda gwanin da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, babbar jam'iyyar hamayya ta wayi gari cikin rigingimun da suka hanata zaman lafiya.
Ayyana gwamna Okowa na Delta a matsayin abokin takarar Atiku ya kara hargitsa rikicin PDP yayin da gwamnonin G5 suka fara kira ga shugaban jam'iyya na ƙasa ya yi murabus.
Duk wani yunkuri na kusoshin siyasa na ganin an rarrashi gwamnonin bai kai ga nasara ba domin sun kafe dole a sauya shugabancin PDP.
Kar Ku Zabi Yan Siyasan Da Zasu Murkushe Yan Ta'adda, Sheikh Gumi
A wani labarin kuma Sheikh Ahmad Gumi Ya Bayyana Cewa Ba Ya Bukatar Samun Shugaban Da Zai Karar da 'Yan Bindiga
A wani karatu da ya gudanar, shehin Malamin wanda ya saba haddasa cece-kuce ya yi katobarar kiran 'yan bindiga da, "Mayakan mu."
A cewarsa, 'yan Najeriya sun fi bukatar shugaban da zai yi sulhu da yan fashin daji, ya masu abinda suke so don a zauna lafiya.
Asali: Legit.ng