Shehu Sani Ta Dura Kan Gwamnonin G-5, Ya Ce Idan Ba Atiku Ba, Su Fadi Wanda Za Su Yi a 2023

Shehu Sani Ta Dura Kan Gwamnonin G-5, Ya Ce Idan Ba Atiku Ba, Su Fadi Wanda Za Su Yi a 2023

  • Yayin da ‘yan Najeriya ke jeran gwamnonin G-5 masu adawa da Atiku su bayyana dan takarar da za su yi a zaben 2023, Sanata Shehu Sani ya aiki musu da sakon shawari
  • Tsohon sanatan na Kaduna da tsakiya a majalisar dattawa kuma jigon PDP ya shawarci fusatattun gwamnonin da su bayyana koma wani ‘shaidanin’ ne da suke so kuma suka sani
  • Karkashin jagorancin gwamna Wike, gwamnonin G-5 na PDP sun ce babu su babu dan takararsu na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar saboda wasu dalilai na cikin gida

Sanata Shehu Sani, tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya kuma jigon jam’iyyar PDP ya ba gwamnonin G-5 na PDP masu adawa da Atiku shawari kan zaben 2023 mai tafe nan kusa.

Gwamnonin G-5 biyar sun bayyana cewa, babu ruwansa da Atiku Abubakar duk da kasancewarsa dan jam’iyyarsu saboda rikicin cikin gida da suke fuskanta a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Ya Yi Wani Abin Ban Mamaki, Ya Sace Zuciyar 'Yan Najeriya da Dama

Gwamna Wike ne shugaban tawagar G-5, kuma suna adawa da Atiku ne da kuma shugabancin PDP, suna neman a tsige shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Shehu Sani ya tabo batun rikicin gwamnonin G-5
Shehu Sani Ta Dura Kan Gwamnonin G-5, Ya Ce Idan Ba Atiku Ba, Su Fadi Wanda Za Su Yi a 2023 | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abin da gwamnonin G-5 ke nema a PDP

Gwamnonin sun ce, Ayu dan Arewa ne daga jihar Benue, don haka dole ya sauka a kujerarsa tunda PDP ta fitar Atiku – shima dan Arewa – a matsayin dan takarar shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun dage cewa, ba zai yiwu a kai manyan kujeru gaba daya ga yankin Arewacin Najeriya ba, don haka suka gama kai don fafutukar neman a sauya wannan lamarin.

Mambobin G-5 sun hada da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benue, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Sakon Sanata Shehu Sani ga gwamnonin G-5

Kara karanta wannan

Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Gwamna Arewa Ya Ayyana Ɗan Takarar Da Zai Marawa Baya a 2023

Yayin da ‘yan Najeriya ke jira don sanin wanda gwamnonin G-5 za su yi a zaben 2023 mai zuwa, Sani ya ba gwamnonin biyar shawari.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, ya kamata gwamnonin su fito su bayyana dan takarar da suke so koma wanene shi.

A wani rubutun na daban, ya ce:

“Allah ya albarkaci kasar nan da ‘yan takarar shugaban kasa kwararru a dimokradiyya kuma masu tarihin juriya ga sukar siyasa, adawa ta siyasa da kitimurmurar siyasa. Ba ma son dan kama-karya mai illa da kuma ra’ayi na daban.”

Idan baku manta ba, gwamnan jihar Benue a nasa bangaren ya fito ya bayyana cewa, Peter Obi yake goyon baya a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel