Kwankwaso Ya Yi Magana a Kan Wa Za a Dauka Tsakanin Tinubu da Atiku a Katsina
- A wajen Rabiu Musa Kwankwaso, babu wani dama-dama tsakanin Asiwaju Bola Tinubu da Atiku Abubakar
- ‘Dan takaran na jam'iyyar NNPP ya ce ‘yan takaran PDP da APC ba za su iya mulki ba domin tsufa ya kama su
- Rabiu Kwankwaso ya dauko wannan magana ne da aka nemi ya zabi daya a cikin wadanda yake takara da su
Katsina - A yayin da ya kai ziyara zuwa jihar Katsina, Rabiu Musa Kwankwaso mai neman mulkin Najeriya a zaben 2023 ya yi hira da manema labarai.
Legit.ng Hausa ta samu faifen bidiyon tattaunawar da aka yi da ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP a gidan rediyon Alfijir FM a yammacin ranar Litinin.
Kamar yadda za a iya saurara a bidiyon da wani Hassan Sani Tukur ya wallafa a Twitter, an yi wa Rabiu Musa Kwankwaso tambaya kan abokan takararsa.
Da aka nemi ‘dan takaran ya zabi mutum guda tsakanin Bola Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP, sai ya nuna babu wani wanda ya fi shi cancanta.
Wa Kwankwaso zai dauka?
Wa za ka dauka tsakanin Bola Tinubu da Atiku Abubakar?
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"To in dauke su, ni kuma in kai kai na ina?"
- Rabiu Musa Kwankwaso
A ce ka zabi guda daga cikinsu:
"To ya za ayi in zabi ko daya? Wadannan fa su kansu matsala ce, kuma sun shiga rubabbun jam’iyya
Dukkaninsu wadannan mutane da ka ke gani, don ba a san gaskiya ne. Su kansu sun san ba za su iya ba. Mutanen nan sun gaji, mutanen nan ba za su iya ba.
Kawai kara-kara ake yi, ana tattara mutane ana tafiya da su. Wasu daga ciki ai ka san harkar rayuwa, idan ka girma, ka kai wani lokaci, sai ka zama yaro."
- Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso yace ayi hattara a 2023
An ji Rabiu Kwankwaso yana cewa da kyar wasu masu neman takaran suke tafiya. Wasu sun soki wadannan kalamai, duk da 'dan takaran bai kama suna ba.
‘Dan siyasar ya yi kira ga Katsinawa da mutanen Arewacin Najeriya su kawo karshen gwamnati mai-ci ganin yadda ake alkawarin za a cigaba da salon APC.
Kwankwaso ya nemi mutane su duba cancanta a zabe mai zuwa, ya ce ko a wajen muhawara ya ce idan aka samu wanda ya fi shi cancanta, to zai bi bayansa.
Na fi su rike kujeru da ilmin boko - 'Dan takaran NNPP
A bangaren ilmin zamani, Kwankwaso ya ce yayin da shi yake da PhD a bangaren ilmin ruwa, sauran ‘yan takaran ba su wuce ilmin sakandare da difloma ba.
Tsohon Gwamnan ya ce ya yi shekaru 17 yana aikin ruwa a Kano, sannan ya yi shekaru 30 ana gwabzawa da shi a siyasa, ya rike mukamai dabam-dabam.
Har a bangaren sanin aiki, ‘dan takaran na NNPP yana tunkaho da ya tserewa kowa, yake cewa kujerar mataimakin shugaban Najeriya ba abin a-zo-a-gani ba ce.
Kwankwaso a Chatham House
A baya an ji labari ‘Dan takaran Shugabancin Najeriya a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi jawabi a gaban Duniya a dakin taro na Chatham House.
A tsakiyar watan Junairun 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso mai harin karbar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyya mai kayan dadi zai je Ingila.
Asali: Legit.ng