Atiku Ya Yi Nadin Mukami, Ya Zabi Budurwa a Matsayin Mai Bada Shawara Kan SDGs
- Paul Ibe ya bada sanarwar cewa Alhaji Atiku Abubakar ya nada Hassana Maina a cikin Hadimansa
- Maina wanda Lauya ce da tayi karatu a Najeriya da Landan, za ta taimakawa takarar Atiku Abubakar
- Lauyar ta yi magana shafin Twitter, ta ce tana neman goyon bayan jama’a wajen sauke nauyin nan
Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nada Hassana Maina ta zama masa mai bada taimako na musamman.
A wata sanarwa da ta fito daga Mista Paul Ibe a ranar Litinin, an ji Atiku Abubakar ya nada Hassana Maina ta rika bada shawara a kan harkokin SDG.
Rahoton The Eagle ya nuna daga cikin ayyukan da Maina za tayi a ofishin Atiku Abubakar, za tayi jagoranci wajen ganin an cin ma manufofin SDG.
Haka zalika wannan matashiya za ta tabbatar manufofin nan sun shiga cikin tsare-tsaren da Atiku yake da shi wajen shugabanci idan ya lashe zabe.
Wacece Hassana Maina?
Sabuwar hadimar ‘dan takarar jam’iyyar adawar Lauya ce kuma kwararriyar sha’ira ce, sannan tayi fiye da shekaru uku tana ayyukan da suka shafi jinsi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hassana Maina tayi fice wajen kare hakkin mata da yaki da cin zarafinsu da ake yi.
Legit.ng Hausa ta fahimci Maina tayi digirinta a bangaren shari’a a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan tayi digirgir na LLM a jami’ar Landan.
A ilminta, jaridar tace Maina ta fi bada karfi a kan abin da ya shafi cigaban al’umma, ta taba samun lambar yabo na musamman daga Future Africa.
A kokari da gwagwarmayar da take yi, Maina ta saba jawabi a tarurrukan gidauniyar Yasmin El Rufai, Purplesilver Community da irinsu Open Arts.
Maina tayi magana
Da take bayani a shafinta na Twitter, ta tabbatar da cewa ta karbi wannan mukami da aka ba ta, kuma a shirye take da tayi aiki da Atiku Abubakar.
Dama tun can, tsohon mataimakin shugaban kasar kuma ‘dan takara a 2023, ya yi alkawarin zai dama da matasa da mata idan ya samu shugabanci.
Bahaushe ya zama Kwamishina
Mun ji labari Majalisar dokokin Kuros Riba ta amince Adamu Uba Musa ya zama Kwamishina bayan girgizar da Ben Ayade ya yi da ya canza sheka.
Mai girma Farfesa Ayade ya kafa tarihi a Jihar da nadin Malam Adamu Musa, wanda asalinsa Bahaushe ne, ya zama Kwamishina a Kudancin Najeriya.
Asali: Legit.ng