2023: Wanda Ya San Sirrin Gwamna Ya Fice Daga APC Zuwa NNPP a Arewacin Najeriya
- Musa Zubairu wanda ya yi wa Muhammad Inuwa Yahaya aiki a baya ya shigo jam’iyyar NNPP
- A zabukan 2011 da 2015, Zubairu shi ne Darektan yakin neman zaben Inuwa Yahaya a Gombe
- ‘Dan siyasar ya tsallaka zuwa bangaren Khamisu Mailantarki, yana goyon bayan ya zama Gwamna
Gombe - Musa Zubairu wanda babban ‘dan siyasa ne a jihar Gombe, ya sauya-sheka daga APC mai mulki zuwa jam’iyyar hamayya ta NNPP.
Rahoton jaridar Aminiya ya tabbatar da cewa Musa Zubairu bar APC zuwa jam’iyyar NNPP wanda mutane suke kira jam’iyya mai kayan dadi.
Musa Zubairu shi ne Darektan yakin neman zaben Muhammad Inuwa Yahaya a lokacin da ya yi takarar kujerar Gwamna a 2011 da 2015.
Yanzu Zubairu yana goyon bayan takarar Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki a zaben 2023. Mailantarki yana neman mulkin Gombe ne a NNPP.
Zubairu zai taimakawa NNPP a 2023
A ranar Talata aka karbe sa da dinbin mutanensa zuwa NNPP, tsohon Darektan kamfen ya yi alkawarin taimakawa jam’iyyar a kowane mataki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Khamisu Ahmed Mailantarki yana kokarin hana Muhammad Inuwa Yahaya zarcewa a kujerar Gwamna.
Za a hana APC tazarce a Gombe?
Babu mamaki ficewar ‘dan siyasar daga APC zuwa NNPP ta taimakawa jam’iyyar hamayyar domin yana cikin wadanda suka san Inuwa Yahaya.
A matsayin wanda ya yi aiki da shi Alhaji Inuwa Yahaya a zabuka biyu domin ganin ya zama Gwamna, Zubairu yana iya kawowa APC cikas a 2023.
Hon. Mailantarki ya wakilci Gombe/Kwami/Funakaye a majalisar tarayya. A zaben 2011 ya fi kowane ‘dan majalisar Arewa maso gabas yawan kuri’u.
Sai a 2019 Yahaya ya yi nasarar doke PDP, ya gaji Gwamna Muhammad Dankwambo.
Ana haka ne sai ga rahoto cewa jam’iyya mai alamar kayan marmari ta karbi wasu mutum uku ‘yan majalisar dokokin jihar Gombe da suka bar APC.
Kwankwaso zai je Chatham House
An ji labari ‘Dan takaran Shugabancin Najeriya a NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi jawabi a gaban Duniya a dakin taro na Chatham House a Ingila.
A tsakiyar watan Junairun 2023, Sanata Kwankwaso mai harin karbar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyya mai kayan marmari zai je Birtaniyar.
Asali: Legit.ng