‘Yan APC Sun Zargi Sanata da Zagon-kasa, Sun Fadi Jam’iyyar da Yake Goyon Baya a Boye

‘Yan APC Sun Zargi Sanata da Zagon-kasa, Sun Fadi Jam’iyyar da Yake Goyon Baya a Boye

  • ‘Yan Concerned Members of Abia North APC sun daina goyon takarar bayan Orji Uzor Kalu a 2023
  • Shugaban kungiyar ya ce Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu bai goyon bayan jam’iyyar APC 10%
  • Kingsley Okorie su na zargin ‘dan majalisar yana goyon bayan takarar ‘danuwansa a wata jam’iyyar

Abia - Sanata mai wakiltar mazabar yankin Arewacin jihar Abia, Orji Uzor Kalu yana fuskantar barazana a tazarcen da yake nema a zaben 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto mutanen yankin Abia ta Arewa su na cewa za su koyawa Sanata Orji Uzor Kalu darasi saboda zargin kitsa zagon-kasa.

‘Ya ‘yan jam’iyyar su na zargin ‘dan majalisar dattawan da son-kai da damuwa da abin da ya shafi dangi da ‘yanuwansa a kan daukacin al’umma.

Masu ruwa da tsaki a yankin sun kira taron manema labarai a garin Umuahia, suka ce yana goyon bayan takarar ‘danuwansa a kan Ikechi Emenike.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Cigaba da Sakin Hannu, An Raba Kyautar Miliyoyi da Ya Je Kamfe a Katsina

A cewar Kakakin masu ruwa da tsakin watau Kingsley Okorie, Sanata Orji Kalu yana goyon bayan ‘dan takaran jam’iyya mai adawa a zaben Gwamna.

Idan zargin Cif Okorie ya tabbata, tsohon Gwamnan na jihar Abia kuma Sanata mai-ci, yana kiran mutanensa su zabi ‘dan takaran APP a zaben Jiha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan APC
Bola Tinubu da Uzor Kalu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ayi shinkafa da wake a 2023

“A tarurruka da da-dama, ya fada mana mu zabi APC a zaben shugaban kasa da majalisar tarayya, amma mu zabi APP a zaben Gwamna.”

- Kingsley Okorie

Babu mu, babu Sanata Orji Kalu

A dalilin wannan zargi, ‘yan kungiyar Concerned Members of Abia North APC suka ce sun janye goyon bayan ‘dan majalisar da suke yi a zabe mai zuwa.

Sannan ‘yan kungiyar sun ce tsohon Gwamnan zai yabawa aya zaki a dalilin cin amanar da ya yi.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Sauya Shekar Mambobin PDP, Fitacciyar Jam'iyya Ta Rushe Kanta, Ta Koma APC

An rahoto Okorie yana cewa za su zabi duk wani ‘dan takara da jam’iyyar APC ta tsaida masu, ban da shi mai neman tazarcen Sanatan Abia ta Arewa.

Kingsley Okorie da mutanensa suna zargin Sanatan da laifin haddasa duk rikicin da ake fama da ita a APC, kuma suka ce bai zuwa taron jam’iyya a Abia.

Akwai matsala idan aka yi sake - INEC

Kun ji labari Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce a cikin shekaru uku da rabi, ‘yan ta’adda sun kai wa INEC hari sau 50 a jihohi 15

Mahmood Yakubu ya ce idan aka kai shekara mai zuwa ba a daina kai wa hukumar INEC hari ba, za a samu matsala wajen shirya zabuka a farkon 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel