Osinbajo Ya ba Marada Kunya, a Karon Farko Tun da Aka Shiga Kamfe, Ya Ziyarci Tinubu
- Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima sun karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa a Abuja
- Farfesa Yemi Osinbajo da kan shi ya kai ziyara ta musamman zuwa gidan ‘dan takaran APC a Abuja
- Bola Tinubu ya ce sun zauna da Osinbajo, kuma sun tattauna kan muhimman batutuwa a kan Najeriya
Abuja - Mai girma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kai wa ‘dan takaran shugabancin kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu ziyara.
Hadimin Farfesa Yemi Osinbajo watau Laolu Akande shi ne ya wallafa hotunan wannan zama da aka ayi da Asiwaju Bola Tinubu a Abuja.
Akande ya fitar da hotuna a shafinsa, ya ce mai gidansa ya kai ziyarar zumunci zuwa gidan ‘dan takaran shugaban kasar a birnin tarayya.
“Yanzu nan Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tsaya kai ziyarar zumunci a gidan Asiwaju Bola Tinubu da ke Abuja.”
- Laolu Akande
Babu jituwa tsakanin Tinubu da Osinbajo?
Vanguard ta ce wasu su na ganin akwai gaba tsakanin Tinubu wanda ya samu takara a APC da kuma mataimakin shugaban kasar Najeriyan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yemi Osinbajo ya kalubalanci tsohon uban gidansa wajen samun tikitin jam’iyya mai mulki a zaben shugaban kasa da za ayi a shekara mai zuwa.
Farfesa Osinbajo bai yi nasara ba, kusan tun lokacin ba a sake ganin shi tare da Tinubu ba, illa ziyarar da ‘dan takaran ya kai masa a Aso Villa.
Idan za a tuna a wancan lokaci, tsohon gwamnan na jihar Legas ne ya kai ziyarar ba-zata zuwa gidan Osinbajo bayan zaben tsaida gwanin APC.
‘Dan takaran ne ya shigo da Osinbajo cikin siyasa a lokacin da ya nada shi Kwamishinan Legas a lokacin da yake kan kujerar Gwamna.
Rahoton ya ce tun bayan zaben fitar da gwani, Osinbajo bai fito karara ya fadawa Duniya yana goyon bayan takarar Tinubu a zaben 2023 ba.
Ko da aka tashi fitar da sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a 2023, babu sunan Farfesa Osinbajo da mai dakinsa.
#Renewedhope23 - Tinubu
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta lura, Bola Tinubu ya fitar da hoton wannan zama a Facebook.
Baya ga Tinubu, mataimakin shugaban kasar ya hadu da Sanata Kashim Shettima, mai neman gaje kujerarsa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Tinubu yake cewa:
"A yammacin nan, ni da abokin gami na, Sanata Kashim Shettima muka karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a gidana na Abuja.
Mun bata lokaci mun tattauna a kan muhimman abubuwan da suka shafi kasa. #Renewedhope23.
- Bola Tinubu
Tinubu ya bada umarnin a tada rigima - PDP
An samu labari Jam’iyyar PDP ta ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wani taro a boye, a nan ya fadawa mutanensa dole su nemi mulki ko ta halin ƙa-ƙa.
Abin da ake zargin Bola Tinubu ya fada a wajen taron Landan shi ne: “Abin da za ayi shi ne a fita a nemi mulki ko ta wani hali, a karbe, kuma a tsere da shi.”
Asali: Legit.ng