Babbar Koma Baya Ga Tinubu Yayin Da Yan APC Sama Da 90,000 Da Wasu Suka Tsallaka Zuwa PDP A Jihar Buhari
- Jam'iyyar hamayya ta PDP ta samu gaggarumin karuwa a jihar Katsina inda ta samu sabbin mambobi kimamin 92,000
- Mambobin sun fito ne daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa da wasu jam'iyyun a yankuna uku na jihar Katsina
- An tarbi sabbin mambobin yayin rali din Atiku Abubakar da aka yi a ranar Talata a Katsina da ta samu halarcin jiga-jigan jam'iyyar
Jihar Katsina - Jam'iyyar PDP a jihar Katsina a ranar Talata ta karbi mambobin jam'iyyar APC da wasu jam'iyyun guda 92,000 a jihar, rahoton Vanguard.
An tarbi wadanda suka sauya shekar a filin wasanni na Muhammadu Dikko a birnin Katsina yayin kamfen din da aka shirya don Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jiga-jigan APC Da Dama Sun Yi Watsi Da Tinubu, Sanwo-Olu, Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga PDP Ta Atiku, Jandor
A cewar direkta Janar ya yakin neman zaben Atiku Abubakar wanda ya fitar da sanarwar, yan APC 49000 sun koma PDP daga Katsina. Yayin da wasu 23000 suka sauya sheka a Funtua sai wasu 19000 a Daura, jimillar wadanda suka sauya sheka 91,000 daga yankuna uku.
Dino ya ce:
"Ya ku jam'a, bari in yi gaggawar sanar da mu cewa muna da wadanda suka shigo jam'iyyar mu daga yankunan Katsina uku.
"Daga yankin Daura muna da mutane 19000 da za suka sauya sheka kuma Alhaji Yahaya Kwande ya wakilce su.
"Daga Funtua, muna da mutane 23000 da suka samu wakilcin Alhaji Baba Yale Yaro kuma a Katsina muna da mutane 49000 daga APC da za su shigo PDP karkashin jagorancin Alhaji Aminu Lawal Mani.
"Amma wanda ya fi muhimmanci cikin masu sauya shekan a nan a yau shine tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina karkashin Gwamna Aminu Bello Masari."
Sanata Iyorchia Shugaban PDP ya tarbi wadanda suka sauya shekan
Da ya ke tarbar masu sauya shekar a hukumance zuwa PDP, shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya yi maraba da dukkan wadanda suka shigo jam'iyyar.
Ya ce sun yi shawara mai kyau da suka hada gwiwa da PDP don ceto kasar daga hannun jam'iyyar APC mai mulki.
Manyan yan APC masu dimbin yawa sun raba jiha da Tinubu da Sanwo-Olu, sun mara wa Atiku da Jandor baya
A gefe guda, daruruwan mambobin jam'iyyar APC a karamar hukumar Epe sun fice daga jam'iyyar sun koma jam'iyyar PDP gabanin babban zaben shekarar 2023.
Gbenga Ogunleye, kakakin kungiyar kamfen din JANDOR4Governor ne ya aika wa Legit.ng hakan cikin wata sanarwa da ke nuna cewa yan APC sun koma PDP a ranar 20 ga watan Disamban 2022.
Sabbin mambobin da suka sauya shekar sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar gwamna na PDP a Legas, Abdulazeez Olaijide Adediran (Jandor) da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP.
Kotu Ta Yanke Wa Matashi Ɗan Shekara 20 Ɗaurin Gidan Yari A Jihar Arewa Saboda Lalata Allunan Kamfen Ɗin Atiku
Asali: Legit.ng