Jiga-jigan APC Da Dama Sun Yi Watsi Da Tinubu, Sanwo-Olu, Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga PDP Ta Atiku, Jandor

Jiga-jigan APC Da Dama Sun Yi Watsi Da Tinubu, Sanwo-Olu, Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga PDP Ta Atiku, Jandor

  • Jam'iyyar APC ta rasa daruruwan mambobinta ga jam'iyyar PDP a Legas
  • Tai Benedict, shugaban PDP a Legas, ya yi maraba da wadanda suka sauya shekan a madadin jam'iyyar a ranar Talata, 20 ga watan Disamba
  • Wadanda suka sauya shekan sunyi alkawarin yi wa dan takarar gwamnan PDP, Abdulazeez Olajide Adediran (Jandor) da Atiku Abubakar aiki

Legas - Daruruwan mambobin jam'iyyar APC a karamar hukumar Epe sun koma jam'iyyar PDP gabanin babban zaben 2023.

Wani sanarwar da Gbenga Ogunleye, shugaban watsa labarai na kamfen din JANDOR4Governor ta aika wa Legit.ng ya nuna cewa mambobin na APC sun koma PDP ne a ranar Talata 20 ga watan Disamba.

Atiku da Jandor
Jiga-jigan APC Da Dama Sun Yi Watsi Da Tinubu, Sanwo-Olu, Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga PDP Ta Atiku, Jandor. Hoto: Atiku Abubakar, LagosforLagos.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Babbar Koma Baya Ga Tinubu Yayin Da Yan APC Sama Da 90,000 Da Wasu Suka Tsallaka Zuwa PDP A Jihar Buhari

Wadanda suka sauya shekar sun ayyana goyon bayansu ga dan takarar gwamna Abdulazeez Olajide Adediran (Jandor) da Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na APC.

Zaben 2023: Abin da yasa muka fita daga APC, wadanda suka sauya sheka suka bayyana

Wadanda suka sauya shekar sun bayyana cewa sun bar APC din ne saboda 'yaudara da cuta mara karewa da ake musu.'

Sun ce yaudarar da tsohuwar jam'iyyarsu ke musu ya janyo matsala gare su kuma zai iya shafar demokradiyya a jihar.

Da ya ke martanin ta, kungiyar kamfen din takarar gwamna na JANDOR/Funke ta bayyana matakin a matsayin karbuwa da goyon baya da PDP, dan takarar gwamna, dan takarar shugaban kasa da sauran yan takarar ke samu daga mutanen Legas.

Mataimakin ciyaman din PDP na Legas ya yi maraba da wadanda suka sauya shekan

Legit.ng ta tattaro cewa mataimakin ciyaman din PDP na Legas, Tai Benedict, ya yi maraba da wadanda suka sauya shekan a madadin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yan Takaran Jam'iyyar NNPP a Jihar Osun Sun Yi Watsi Da Kwankwaso, Sunce Tinubu Zasu yi

Benedict ya jinjinawa wadanda suka sauya shekan saboda "karfin gwiwan su na barin jam'iyyar da ke yaudararsu tare da shigowa PDP don ceto jihar daga mulki mara kyau na tsawon shekaru 23."

Ya basu tabbacin za a kare musu hakkinsu kuma za a kula da su tamkar tsaffin yan jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel