Atiku Ya Cigaba da Sakin Hannu, An Raba Kyautar Miliyoyi da Ya Je Kamfe a Katsina

Atiku Ya Cigaba da Sakin Hannu, An Raba Kyautar Miliyoyi da Ya Je Kamfe a Katsina

  • ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci Katsina
  • Wazirin na Adamawa ya bada kyautar N50m ga wadanda matsalar rashin tsaro ya shafe su a jihar
  • A baya Atiku ya yi rabon irin wannan kudi yayin da ya je yawon kamfe a Jihohin Kano da Bayelsa

Katsina - Alhaji Atiku Abubakar mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya bada sanarwar gudumuwar kudi a jihar Katsina.

Daily Trust ta ce Atiku Abubakar ya yi alkawarin kyautar Naira miliyan 50 ga wadanda matsalar rashin tsaro ya ta same su a garuruwan jihar.

Ba wannan ne karon farko da ‘dan takaran ya raba makudan kudi a lokacin da ya ke yawon yakin zabe ba, an yi haka a Jigawa, Kano da jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Da Okowa Sun Ziyarci Mahaifiyar Marigayi Yar'adua a Katsina, Hotunan Sun Ja Hankali

‘Dan takaran shugabancin kasar ya sanar da hakan yayin da shi da tawagarsa suka ziyarci Mai martaba Abdulmuminu Kabir Usman a ranar Talata.

Atiku ya je fadar Abdulmuminu Kabir Usman

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya kai ziyarar ban girma ga Dr. Abdulmuminu Kabir Usman domin a tofawa takararsa albarka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto Atiku yana cewa ya je wajen Sarkin ne domin neman shawara, addu’o’i da albarka.

Atiku
Atiku a Fadar Abdulmuminu Kabir Usman Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

A jawabinsa, ‘dan takaran kujerar shugaban kasar jam’iyyar hamayyar ya nuna ya damu da yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a bangarorin Najeriya.

Atiku ya yi alkawarin idan ya dare kan kujerar shugaban kasa a Mayun 2023, zai magance rashin tsaro da kuma matsin tattalin arzikin da ake fuskanta.

Mai martaba ya ji dadi

Shi kuma da yake maida martani, Sarkin na Katsina ya ce ya ga haske a takarar da Atiku Abubakar yake yi a 2023 a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Kunno a PDP Yayin da Atiku Abubakar Da Tawagarsa Zasu Shiga Katsina Yau

Dr. Abdulmuminu Kabir Usman ya ce ya ji dadi da Atiku yake maganar tsaro da tattalin arziki domin su ne abubuwan da suka sa shi jinya a gadon asibiti.

Tawagar Atiku a Katsina

Abokan tafiyar Atiku sun hada da: Ifeanyi Okowa; Yakubu Lado Danmarke; Aminu Waziri Tambuwal. Jaridar This Day ta fitar da wannan labari dazu.

Akwai irinsu Sule Lamido, Malam Ibrahim Shekarau, Ahmed Muhammad Makarfi, Mu’azu Babangida Aliyu, Yakubu Dogara, Dino Melaye da sauransu.

Yadda LP za ta ci zabe

An ji labari lissafin da magoya bayan Peter Obi suke yi shi ne, NNPP ta hannun Rabiu Musa Kwankwaso za ta birkita lissafin PDP da APC a yankin Arewa.

Idan aka je Kudancin Najeriya,Peter Umeh ya ce Peter Obi zai hana Atiku Abubakar sakat, sannan jam’iyyar NNPP ba za ta iya samun karbuwa a Kudu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng