Hotunan Atiku Da Okowa Yayin da Suka Ziyarci Mahaifiyar Marigayi Yar’adua, Hajiya Aya Dada a Katsina
- Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP da abokin tafiyarsa, Ifeanyi Okowa sun kai ziyarar ban girma ga Hajiya Aya Dada
- Yan takarar na PDP sun ware lokaci sun je ganin mahaifiyar marigayi shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua yayin da suka je kamfen a jihar Katsina
- Yan Najeriya da dama sun yi farin ciki da ganin dattijuwar matar yayin da suka yi mata addu'an tsawon rai cikin koshin lafiya
Katsina - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa sun ziyarci mahaifiyar marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa Yar’adua a Katsina.
Yan takarar sun ziyarci Hajiya Aya Dada ne a ranar Talata, 20 ga watan Disamba yayin da suka je jihar don yakin neman zabensu.
Da yake wallafa hotunan ziyarar tasu a shafinsa na soshiyal midiya, Okowa ya bayyana dattijuwar matar a matsayin mai zuciyar alkhairi inda ya roki Allah da ya albarkaceta tare da kara mata tsawon rai.
Ya rubuta:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Hajiya Aya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Yar’adua da Tafida Shehu Musa Yar’Adua ta kasance uwa ga mutane da dama. Babban zuciyanta ya tarbi shugabanni da dama daga jam’iyyun siyasa daban-daban.
“Wannan ne dalilin da yasa a safiyar yau, nake alfaharin jerawa da dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar wajen kaiwa Hajiya Aya Dada ziyara a mahaifarta da ke Katsina.
“Muna rokon Allah ya ci gaba da yi mata albarka da kuma barinta a raye. Ameen!”
Ga wallafar tasa a kasa:
Jama’a sun yi martani
Chiedu Ikechukwu ya yi martani:
"Hakan ya yi kyau kuma ya dace, Jihar Katsina sun gaji da wahala da matsin rayuwa na APC sannan suna bukatar AtikuOkowa don ceto su, PDP ta shirya ceto Najeriya mulkin zalunci na APC, Katsina ta shirya, Najeriya ta shirya, AtikuOkowa sun shirya tsaf."
Emmanuel Junior Zakka ya ce:
"Zuciyata ta yi nauyi a nan. Allah ya ja da ran kaka cikin koshin lafiya. Allah ya albarkaci mai hada kan kasa kan wannan ziyarar.
"Ba za ta mutu ba har sai ta shaida rantsar da ku, da izinin Allah."
Rukevwe Inije ta ce
"Wow, godiya ga AtikuOkowa da kuka nuna kauna ga ahlin Yar'adua, na san mahaifiyar tsohon shugaban kasar Najeriya za ta yi farin ciki sosai da ganin tawagar ceto. AtikuOkowa sun damu saboda a matsayin daya za mu cimma abubuwa. Ku zabi AO2023."
Omoh Eduvie ta ce:
"Danta, tsohon shugaban kasar Najeriya ya kasance mutumin kirki wanda ke nufin yan Najeriya da alkhairi kafin mutuwa ta dauke shi, ta tarbiyantar da shi sosai, mama Allah ya ja da ranki cikin koshin lafiya."
Shema ba zai yiwa Atiku Kamfen ba
A gefe guda, mun ji a baya cewa tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema basa tare da yakin neman zaben Atiku Abubakar saboda banbancin da ke tsakaninsu da dan takarar gwamnan PDP a jihar, Sanata Yakubu Lado Danmarke.
Asali: Legit.ng