APC Ta Caccaki PDP da Atiku Kan Zargin Kullalliya Game da Sunan Tinubu Na Gaskiya
- Gabanin babban zaben 2023, majalisar gangamin kamfen APC na ci gaba da martani ga dukkan kalubale daga ‘yan adawa
- A wannan karon, majalisar ta kamfen APC ta caccaki PDP da ‘yan takararta bisa tabo batun da ya shafi sunan dan takarar shugaban kasan APC Tinubu
- A bangare guda, majalisar ta yi bayani game da Tinubu, ta ce babu wata kitimurmura tattare da dan takararsu na shugaban kasa
FCT, Abuja – Majalisar gangamin kamfen din Tinubu/Shettima a jam’iyyar APC (PCC) ta caccaki abokin hamayyar Tinubu a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bayan da wani batu da ya taso kan ainihin sunan Tinubu.
Jam'iyyar PDP da dan takararta a baya sun sun dauko wani batun da ke dasa alamar tambaya kan gaskiya sunan Tinubu, lamarin da ya jawo cece-kuce, rahoton TheCable.
A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samo a ranar Litinin, 19 ga watan Disamba, majalisar kamfen APC ya yi martani ga batun Atiku na tambayar bahasin gaskiyar sunan Tinubu da ‘mataccen zargi’.
Majalisar ta APC ta ce, Bola Ahmad Tinubu ya maida hankalinsa ne ga yadda zai ci zaben 2023 bai wai sauraran babatun ‘yan adawa ba da ke kokarin bata masa suna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A bangare guda, APC ta ce tuni aka wanke Tinubu daga dukkan zarge-zarge, ciki har da batutuwan da ke gaban kotu da ke kalubalantar cancantarsa.
Ba mu da lokacinku, APC ga PDP
Hakazalika, PCC ta ce bata yi mamakin abin da PDP ta fada ba, saboda a kage jam’iyyar adawar take ga yadda za ta shafa kashin kaji ga abokan hamayya don samun karbuwa a idon ‘yan Najeriya.
A cewar wani yanki na sanarwar:
“Babu dadi yadda jam’iyyar da dan takarar na shugaban kasa, Atiku Abubakar, suka zabi dawo da mataccen zargi, tare da sanin cewa, wannan zaben ma zai kubce musu.”
Zaben APC zai sake jefa ‘yan Najeriya a matsala, inji malamin addini
A wani labarin kuma, wani fitaccen malamin addinin kirista a Najeriya, Primate Elijah Adoyele ya bayyana kadan daga rikicin da ke tattare da zaban APC.
A cewarsa, zaban APC a wurin ‘yan Najeriya zai zama babban tashin hankali ga ci gaban kasar, musamman duba da yadda jam’iyyar ke shirin ci gaba da mulki ta kowane hali.
Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su guji APC, kana ya ankarar da Peter Obi da Atiku Abubakar kan cewa, kada su bari Tinubu ya lashe zaben badi.
Asali: Legit.ng